Neymar da Mbappe suna manyan ‘yan wasan kungiyar yanzu wadanda ake ji da su, duk da cewa Mbappe matashi ne amma yanayin taimakon da yake bawa kungiyar yasa ya zama dan wasa mai tasiri kuma mai fada aji.
Yanzu babban abinda sabon mai koyarwa Mauricio Pochettino zai nema a kungiyar daga wajen ‘yan wasa bai wuce hadin kai daga wajen shahararrun manyan ‘yan wasan kungiyar ba, domin ganin hya samu nasara.
Manyan ‘yan wasan kungiyar, Neymar da Kylian Mbappe suna daya daga cikin wadanda zasu taka muhimmiyar rawa wajen nasarar sabon mai koyarwa duba da irin tasirin da suke da shi a kungiyar saboda kwarewarsu da kuma girmansu a idon duniya.
Tuni wasu rahotanni daga kasar Ingila suka fara bayyana cewa korar da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yiwa kociyan kungiyar Thomas Tuchel zata iya hana dan wasa Kylian Mbappe komawa Real Madrid a karshen kakar wasa idan har yaga kamun ludayin Pochettino.
Thomas Tuchel na daga cikin mutanen da suka taimakawa kungiyar ta PSG tsawon lokacin da ya share da babbar kungiyar PSG kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar tun bayan komawarsa daga kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus.
Rashin lashe kofin zakarun Turai ya sa magabatan kungiyar ta PSG suka yanke shawarar korar Tuchel bugu da kari a wannan kakar wasan kungiyar bata buga abin arziki a gasar lig one ta kasar Faransa kuma tuni kungiyar ta shiga tattaunawa da wani makusancin Tuchel, dan kasar Argentina Mauricio Pochettino.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa tafiyar mai koyarwa Tuchel, wanda basa shiri da Mbappe zata iya sanya dan wasan ya zauna a kungiyar duk da cewa wasu daga cikin manyan kungiyoyi ciki har da Real Madrid da Liberpool suna bibiyar dan wasan dan asalin kasar Faransa.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi alkawarin sayan dan wasa Mbappe idan an kammala kakar wasan bana wanda hakan ne yasa kungiyar bat sayi dan wasa ko daya ba a kasuwar data gabata saboda tana tara kudin sayan Mbappe.
A kwanakin baya dan wasan shima ya bayyana cewa bashi da burin ci gaba da zaman kungiyar kuma yana fatan a karshen kakar wasa zai koma daya daga cikin kungiyoyi manya a nahiyar turai.
Shi ma dan wasa Neymar, wanda baiji dadin korar da akayiwa Tuchel ba, yana bukatar tsayawa domin karatun ta nutsu akan yanayin da kungiyar zata kasance nan gaba duba da har yanzu ba’a san wanda kungiyar zata dauka ba.
A kwanakin baya Neymar ya bayyana cewa zai iya barin kungiyar ta PSG idan har shugabannin kungiyar ba suyi kokarin sayo dan wasa Messi ba wanda yake shirin barin Barcelona a karshen kakar wasa ta bana.