Dole A Saka Na Hannun Daman Buhari A Sunayen Ɓarayin Gwamnati

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa, dole ne a sanya har na hannun daman Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a jerin sunayen da gwamnatin tarayya za ta saki na ɓarayin gwamnati, ya na mai yabawa da wannan mataki da gwamnati ke shirin ɗauka na yin terere.

A ta bakinsa ya yi habaicin cewa, “ba ’yan lema kaɗai ya dace a saka a jerin sunayen ba, har ma da ’yan tsintsiya da kuma na hannun fadar shugaban ƙasa.”

Sanata Sani, wanda ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Facebook, ya ce, hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke na bayyana sunayen abin a yaba ne. Don haka ya na fatan ba za a taƙaice shi a kan ’yan bora kurum ba, za a haɗa da dukkan ’yan mowa masu kashi a gindi

Sanatan ya na mayar da martani ne kan rahotannin da ke tabbatar da cewa, Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga ma’aikatun tarayya, sassa da hukumomi da su tattara jerin sunayen jami’an gwamnati waɗanda su ka yi ta’annati da kuɗaɗen al’umma kuma waɗanda a ka amso dukiyoyi a hannunsu, domin bayyana su.

Ministan shari’a kuma antoni janar na tarayya, Alhaji Abubakar Malami, SAN, ne ya bayyana hakan a wani taro da ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta gudanar a cikin makon nan, inda ya yi ƙarin haske da cewa, matakin ya biyo bayan hukuncin da kotu tarayya da ke Lagos ta yanke ne, wanda ta umarci gwamnatin tarayya da ta buga jerin sunayen ɓarayin da kuma yawan adadin kuɗin da a ka amso daga hannunsu.

Irin waɗannan kalamai na Sanata Sani ba su ne na farko ba da su ka taɓa jagwalo abin cece-kuce, inda ko a kwanakin baya an ruwaito matar shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ta na yin shaguɓe kan wata magana da ya furta.

 

 

Exit mobile version