Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Domin Karfafa Tsaron Iyaka, NIS Ta Kaddamar Da Sansaninta Na Belel

An Jinjina Wa Shugabancin Babandede A Taron

Shugaban NIS Muhammad Babandede (a tsakiya) tare da sauran manyan bakin da suka halarci kaddamar da sansanin na Belel a Jihar Adamawa.

A cigaba da kokarin da take yi na tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasa da bakin-haure ke amfani da su, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta kaddamar da sansanin jami’anta na kan-iyaka a Belel da ke Jihar Adamawa.

Shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da sansanin a ranar Juma’a 12 ga Fabarairun 2021.

Kaddamar da sansanin na Belel ta sake nuna cewa Babandede da gaske yake yi a kan alwashin da ya dauka na tabbatar da karfafa tsaron iyakokin kasar nan, inda zuwa yanzu sansanin na Belel ya zama cikon na 15 da shugaban ya samar.

Da yake jawabi a wurin kaddamarwar, CGI Babandede ya gode wa manyan mutanen da suka halarci taron musamman wakilin Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri saboda goyon bayansa, da shugaban karamar hukumar Maiha Alhaji Idi Amin, da mai martaba Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu, da Danburram Mubi Sarkin Belel, bisa kyakkyawar tarba da bayar da wurin masauki ga jami’an hukumar.

Shugaban na NIS ya sake jaddada kudirinsa na ziyartar kowane sansani na jami’an hukumar domin kara musu kwarin gwiwar aiki da kuma magance abubuwan da ke addabarsu da kansa ba sako ba, yana mai cewar, “hakki ne a kaina in ziyarci jami’aina a duk inda aka ajiye su, domin nuna shugabanci nagari.”

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS DCI Sunday James, ta yi bayanin cewa, shugaban karamar hukumar Maiha Alhaji Idi Amin ya yaba wa CGI Babandede saboda kyakkyawan shugabancinsa da hangen nesa wadda ta albarkarsu aka samu bunkasar ababen more rayuwa da kayan aiki a sassan hukumar da nufin kyautata jin dadi da yanayin aikin jami’ai.

Idi Amin wanda ya kasance tsohon jami’in NIS ya bayyana irin gagarumin sauyin da ya gani a sassan ayyukan NIS ga jama’a a cikin kankanen lokaci da hawa shugabancin Babandede, da nadinsa ya samu sambarka a ciki da wajen kasar nan.

 

 

Exit mobile version