Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa ma’aikatar harkokin Matasa a Abuja (FCT), a cewar Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike. An bayyana hakan ne yayin wata ganawa da mazauna ƙaramar hukumar Bwari, a wani yunkuri na Minista Wike na ci gaba da samar da zaman lafiya a yayin da ake shirin gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Wannan ganawar ta biyo bayan wasu tattaunawar a baya da aka yi a Gwagwalada, da Kuje, da Kwali, da ƙaramar hukumar birnin Abuja (AMAC), da Abaji don hana matasa shiga zanga-zangar.
- Zanga-Zanga: Sojoji Sun Karɓe Iko Da Tsaron Hanyar Shiga Abuja
- An Tona Asirin Masu Yi Wa Matatar Dangote Zangon Ƙasa
Wike ya amince da wannan buƙata ne a lokacin da matasan AMAC suka gabatar masa da ita, wanda ya yi alƙawarin tattaunawa da Shugaba Tinubu. Ministan ya tabbatar da amincewar a lokacin ganawar a Bwari, yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da haɗin kan matasa da bunƙasa su. Ya yaba wa matasan bisa kin shiga zanga-zangar da ake shirin yi, yana ganin wannan mataki na nuna hazaƙa da goyon bayan gwamnati ne. Wike ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa za a ci gaba da inganta ababen more rayuwa, tare da kammala ayyukan hanyoyi a garuruwan wajen FCT nan da Disamba 2024.
A nasa jawabin, Mista Ezekiel Dalhatu, wanda ya wakilci ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta Matasa da haɗin gwuiwar dukkan ƙungiyoyin matasa a FCT, ya tabbatar da cewa matasa sun yanke shawarar shiga tattaunawa maimakon zanga-zanga.
Ya jaddada muhimmancin tattaunawa mai ma’ana da gwamnati don magance matsalolinsu. Shugaban ƙaramar hukumar Bwari, Mista John Gabaya, ya yi kira ga matasa da su rungumi tattaunawa, yana mai tabbatar wa Wike da goyon bayan mazauna FCT.
An kammala zaman ne da gabatar da hoton girmamawa na Wike daga matasa da sauran masu ruwa da tsaki.