Yadda kasar Sin ta dorad da ba da fifiko ga kirkire-kirkire, da bunkasa zuba jari a sashen bincike da samarwa, da kyautata yanayin kare ikon mallakar fasaha, sun taimaka mata wajen ci gaba da zama jagora a duniya da ke da mafi akasarin rukunonin fasahohin kirkire-kirkire, kamar yadda hukumar kula da harkokin kare ikon mallakar fasaha (IP) ta kasar Sin ta bayyana, a yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya Jumma’a.
Mai magana da yawun hukumar Du Yu, wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa wata tambaya game da sabon mizanin fasahar kirkire-kirkire na duniya da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya (WIPO) ta fitar, ya kara da cewa, mizanin ya nuna cewa, yanzu kasar Sin ce take da manyan rukunan kirkire-kirkire guda 24 daga cikin guda 100 da ake da su a duk duniya, inda ta ci gaba da rike matsayinta na zama kan gaba a duniya. Haka kuma, rukunin kirkire-kirkiren fasaha na Shenzhen-Hong Kong-Guangzhou ya kai matsayi na daya a karon farko.
Du ya yi nuni da cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a sashen bincike da samarwa ya karu zuwa yuan tiriliyan 3.6, kwatankwacin kimanin dalar Amurka biliyan 507 a shekarar 2024, wanda ya zama na biyu a duniya. Har ila yau, ya kara da cewa, zuwa watan Yunin da ya gabata, adadin lasisin hakkin mallakar fasahar kere-kere na cikin gida na kasar Sin ya kai miliyan 5.01, inda kamfanoni ne suke da guda miliyan 3.73 daga cikinsu, lamarin da ke nuna ci gaba da samun bunkasar fasahar kirkire-kirkiren da kamfanonin ke yi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp