• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dr. Maryam Yola Ta Zama Farfesa Mace Ta Farko Kan Magungunan Gargajiya Da Al’adun Hausa

Mutane da dama ne suka taya Dr. Maryam Mansur Yola murnar zama Farfesa kan magungunan gargajiya da al'adu a shafukan sada zumunta.

by Muhammad and Naziru Adam Ibrahim
10 months ago
Dr

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano, ta amince da ɗaga darajar Dr. Maryam Mansur Yola, ta Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, da ke Jami’ar zuwa matsayin Farfesar Magungunan Gargajiya da Al’adu, kamar yadda wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Juma’a 27 ga Disamba, 2024 ta bayyana.

Farfesa Maryam Yola, ‘yar asalin ƙaramar hukumar Kano Municipal, ita ce mace ta farko a tarihi da ta zama farfesa kan magungunan gargajiya da al’adun Hausa, kuma malama ce da ke koyar da kwasa-kwasan Al’adun Bahaushe da ta koyar da ɗumbin ɗalibai a matakan ilimin daban-daban a ciki da wajen Nijeriya.

  • Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani
  • Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita

Farfesa Yola, mace ce da ta yi fice kan bincike a fannin magungunan gargajiya tun daga digirinta na farko, inda ta yi akan darussan Hausa a shekarar 1990, ta yi digirinta na biyu kan al’adun Bahaushe a shekarar 1997. Farfesa Yola ta kuma kammala karatunta na digiri na uku a shekara ta 2017, duka a Jami’ar Bayero. Kazalika, Farfesar ta yi babbar difiloma kan harkokin koyar da ilmi (PDE) a Kwalejin Shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal) da ke Kano, inda ta kammala a shekarar 2015, ta kuma samu ƙarin wasu takardun shaidar ilimi a wasu kwasa-kwasai da dama.

Baya ga takardu da maƙalu masu tarin yawa da ta gabatar kan magungunan gargajiya a jami’o’i da makarantu da wuraren tarukan ilimi daban-daban a ciki da wajen Nijeriya, ta duba aikin ɗalibai masu tarin yawa a matakin digiri na ɗaya da na biyu da na uku a Jami’ar Bayero da wasu Jami’o’i a Nijeriya.

Farfesa Yola, ta kuma riƙe muƙamai da dama a matakin gwamnatin tarayya da jiha da wasu kungiyoyin siyasa da jami’a da ƙungiyoyin ci gaban al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Farfesa Mansur Yola, mamba ce a Ƙungiyar malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), kazalika mamba ce a Ƙungiyar Mata ta (ASFECOM), da kuma hukumar da ke bayar da shaidar malanta ta Nijeriya (TRCN).

A zamanin mulkin Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ta riƙe Shugabar Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta Jihar Kano daga 2008 zuwa 2011, da sauran muƙaman gwamnati da siyasa da dama a matakai daban-daban.

Ana sa ran ɗaga darajar Fafesar zuwa wannan mataki zai ƙara mata himma da ƙwarin gwuiwar ci gaba da bayar da gudunmowa wajen inganta harkokin magungunan gargajiya a Nijeriya, ta hanyar amfani da ɗimbin ilimi da ƙwarewarta a fannin, tare da bunƙasa al’adun Hausa, da cike giɓin da ake da shi a ɓangarorin magungunan gargajiya da al’adun Hausa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Yankin Xinjiang Na Kasar Sin Ya Kammala Aikin Shimfida Rami Mafi Tsawo A Duniya

Yankin Xinjiang Na Kasar Sin Ya Kammala Aikin Shimfida Rami Mafi Tsawo A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

October 24, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

October 24, 2025
Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.