Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
Hukumar Kula da Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta fadakar da ‘yan Nijeriya game da shirye-shiryen da wasu masu aikata laifuka ke yi na kai hare-hare a wuraren taruwar jama’a, a inda miyagun ke shirin farwa muhimman wurare.
Hare-haren da aka tsara bisa ga ganin hukumar, za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da abubuwan fashewa, harin kunar bakin wake da sauran muggan makamai.
Don haka ne ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani bakon abu da ake zargi a kusa da su, ga jami’an tsaro na kusa da su.
A nata bangaren, Hukumar ta bayyana cewa, “tana hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an samar da isassun matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Don ci gaba da dakatar da wannan manufar, hukumar ya samar da wadannan lambobin don amsa gaggawa: 08132222105 da 09030002189.
Har ila yau, tana amfani da wannan damar don bayyana yanar gizon ta na mu’amala, www.dss.gob.ng, don tallafa wa sadarwar jama’a.
A na kuma karfafa kowa da ya yi amfani da wadannan dandamali da makamantan su wadanda hukumomin da ke da alaka ke bayarwa don isa ga lokaci da kuma wadatar da su, (hukumomin tsaro) da bayanan da ake bukata.
Amma kuma hukumar ta shawarci masu shirin haifar da hargitsi da lalata zaman lafiyar jama’a da su guji yin hakan domin hakan ba zai tsayar da komai ba wajen kamo su da gurfanar da su a gaban kotu.
Yayin da ya ke bai wa ‘yan kasa da mazauna kasar tabbacin tsaron su a lokacin da kuma bayan lokutan bukukuwan, Babban darakta, ma’aikatar Jiha, Alhaji YM. Bichi, tare da ma’aikatansa, su na yi wa kowa barka da Bukukuwan Kirsimeti, da na sabon shekarar 2021.