Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta kama jagoran Inyamurai mazauna rukunin gidajen Ajao a Jihar Legas.
Fredrick Nwajagu ya yi barazanar gayyatar ‘yan kungiyar Biyafara (IPOB) zuwa Legas don kwato wa al’ummar Inyamurai kadarorinsu a jihar.
- Karamin Ministan Man Fetur Timipre Sylva, Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
- Mutum 50 Suka Amfana Da Zakkar Da Wani Bawan Allah Ya Fitar A Kaduna
Leadership Hausa ta ruwaito cewa, an kama jagoran Inyamurai ne da safiyar ranar Asabar a wani samamen hadin gwiwa tsakanin jami’an DSS da ‘yan sanda.
Bayanai sun nuna cewa jami’an tsaron sun nemi kama shi a fadarsa, amma sai ya gudu, inda suka rika bin sawunsa har suka kama shi a wani otal.
A ranar Juma’a ne, Mista Nwajagu mai shekara 49 ya yi barazanar gayyatar ‘yan IPOB zuwa Jihar Legas domin kare ‘yan kabilar Inyamurai mazauna jihar daga hare-haren da ya ce ana kai musu.