Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta saki tsohon darakta-janar na kwamitin yakin zaben Peter Obi, Doyin Okupe, bayan da ta kama shi.
An ruwaito cewa an kama Okupe ne a ranar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
- Jam’iyyun APC Da NNPP Na Mayar Wa Da Juna Martani Kan Sabbin Masarautun Kano
- Ɗan China Da Ake Zargi Da Kisan Ummita Ya Ce Naira Miliyan 60 Ya Kashe Mata
Lauyansa, Tolu Babaleye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Okupe na kan hanyarsa ta zuwa Landan lokacin da aka kama shi.
Da yake magana bayan an sake shi, Okupe ya ce EFCC ta nemi afuwar wannan kuskuren.
“An kama ni kuma an tsare ni a filin jirgin sama na Legas a safiyar ranar 12 ga watan Janairu a kan hanyata ta zuwa Birtaniya don neman lafiya.
“Na bar ofishin EFCC inda manyan jami’an Legas da na Abuja suka ba ni hakuri kan kuskuren da aka yi.”