Dubban matasa ne suka cika titunan birnin Kano ranar Alhamis, inda suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna goyon bayansu ga kwamishinan ‘yansandan jihar, CP AI Bakori.
Masu zanga-zangar wadanda akasarinsu ‘yan asalin jihar Kano ne, suna dauke da kwalaye da alluna dauke da taken “A bar mana CP” “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ka kyale mana CP”.
- Alaafin Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Kama Masu Kashe Kashe A Kwara
- PENGASSAN Ta Musanta Janyewa Daga Yajin Aiki, Ta Gargaɗi Dangote
Zanga-zangar na zuwa ne biyo bayan kiran da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi mai cike da cece-kuce a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata.
A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.
Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp