Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a jiya ya bayyana cewa komai na rayuwarsa ya faru ne ta hanyar bazata wanda ya hada da zamansa a matsayin shugaban kasa a lokacin mulkin soja da kuma shugaban kasar Nijeriya a lokacin dimokuradiyya.
Tsohon shugaban kasar wanda ya zama bako na musamman a wani shiri na gidan rediyo mai zaman kansa a Abeokuta, ya ce in ban da noma da aka haife shi a ciki, wasu sun faru ne ta hanyar bazata, inda ya kara da cewa yana alfahari kasancewarsa manomi.
- Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Sun Roki Manyan Kasashen Duniya Su Kawo Musu Dauki
- ‘Yan Sandan Birnin Milan Sun Ba Wa Dan Wasa Bukayoko Hakuri
Da yake amsa tambayoyi daga tsohon kyaftin din Super Eagles, Segun Odegbami, wanda ke jagorantar shirin Obasanjo ya jaddada cewa ba daidai ba ne kowa ya kira kansa manomi.
Ya ce, “Ba na so kalmar da kuka yi amfani da ita, ‘ soyayya da noma’, ni manomi ne. Me kuke nufi da soyayya? Duk abin da na yi a rayuwata ta hanyar bazata ne. Abin da ba bazata bane, shi ne noma. Duk sauran abubuwan da na kasance cikin bazata ne.
“Ka san yadda na fara. An haife ni a kauye. Na je makaranta ne bisa bazata. Mahaifina ya ce, ‘ba za ku samar da komai na daban ba? Shi yasa na shiga harkar noma.
“Idan aka duba kasashen da suka ci gaba, sun ci gaba ne a fannin noma. Na farko, don samar da abinci, na biyu don sarrafa abin da suke samu daga gonakinsu. Na uku, a ba da shi a matsayin fitar da shi zuwa kasashen waje, wanda shi ne manufar samun kudin waje.
“Kuma hanyar samar da ayyukan yi ne ga matasa”.
Obasanjo wanda ya shawarci matasan Nineriya da su karbi mukaman shugabanci a yanzu, ya bukace su da kada su bari wani ya yaudare su da sunan su manyan gobe ne.
Ya ce wasu gurbatattun shugabanni za su ruguza abin da ake kira gobe idan matasa suka kasa tashi tsaye su dauki makomarsu a hannunsu.
“Shawarata ga matasan Nijeriya ita ce, kada ku bari wani ya ce muku ku ne shugabannin gobe. Za ku jira goben kafin ku karbi ragamar shugabancin, to gobe ba za ta zo ba. Wannan lokaci ne da ya kamata matasa su tashi su tabbatar da hakan,” inji shi.