• English
  • Business News
Friday, September 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa

by Sani Anwar
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kusan shekara guda bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a matsayin doka, mafi yawancin jihohi a halin yanzu; sun amince da fara biyan mlaman makaranta da ma’aikatan kananan hukumomi.

Da farko dai, jihohi da dama sun amince da biyan kudi kadan, bisa la’akari da karancin kudade da ake fama da su, yayin da wasu suka takaita biyan ma’aikatan gwamnati, amma ban da malamai da ma’aikatan kananan hukumomi.

  • Matsin Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje
  • Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya

Sai dai, wani bincike da LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa; idan aka cire wasu jihohi kadan, mafi yawancin jihohin a halin yanzu na biyan wannan mafi karancin albashi ga ma’aikatansu. Musamman Jihohin Borno, Kaduna, Nasarawa, Yobe da kuma Zamfara har yanzu ba su sanya jerin ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare a cikin tsarin albashin ba.

Kaduna: Ana Kan Tantancewa

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa, za ta dauki matakin biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare bayan kammala tantance ma’aikatan.

Labarai Masu Nasaba

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Mai bai wa Gwamna Uba Sani shawara kan harkokin kwadago, Adamu Samaila ne ya shaida wa wakilinmu cewa; nan bad a jimawa ba gwamnati za ta karbi rahotan tantance ma’aikatan da kuma yadda za a daidata albashin nasu.

Samaila ya kara da cewa, “A mako mai zuwa ne za mu gana da wanda yake kula da aikin tantancewar, domin samun sakamakon rahoton albashin ma’aikatan.”

Zamfara: Ba A Aiwatar Da Biyan Dari Bisa Dari Ba

A Jihar Zamfara, gwamnati ba ta aiwatar da fara biyan sabon mafi karancin albashin ga ma’aikatanta ba. Guda daga cikin manyan jami’an gwamnatin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa; mafi karancin albashin, zai fi mayar da hankali ne a kan ma’aikatan da ke mataki na uku zuwa mataki na bakwai, wajen biyan cikakken albashin na Naira 70,000, sabanin wadanda ke kan mataki na 8 zuwa sama.

Shugaban kungiyar malamai na Nijeriya (NUT), Yahaya Mafara ya bayyana cewa; ana kan yin gyara kan batun biyan wannan albashi na ma’aikata.  

Nasarawa: Na Biyan Kashi 40 Cikin 100

A Jihar Nasarawa, har yanzu ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makarantun gaba da sakandare, bas u samu cikakken wannan mafi karancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Nijeriya (NULGE) na jihar, Kwamared Adamu Sharhabilu, ya shaida wa LEADERSHIP cewa; a halin yanzu ma’aikata na samun kashi 40 cikin 100 na karin mafi karancin albashin, ya kuma bayyana fatansa na fara aiwatar da biyan cikakken albashin na Naira 70,000 daga nan zuwa karshen watan Yuni.

Haka zalika, ya kuma alakanta wannan gazawar da batun kason kudaden kananan hukumomi da ake yankewa daga asusun gwamnatin tarayya.

Sharhabilu ya bayyana cewa, “Ka san karamar hukuma, ba kamar jiha ba ce, ana cire kashi biyar cikin dari na Sarakuna, kashi daya na horar da hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi, kashi daya na babban mai bincike, kashi daya na ma’aikatar kananan hukumomi da kuma kashi daya na hukumomin lafiya.

Don haka, abin da ya yi saura bayan an cire wadannan, ba zai isa a biya wannan mafi karancin albashi ba. Amma, mun gana da hukumomin da abin ya shafa kan lamarin tare da dagewa wajen ganin an biya cikakken wannan mafi karancin albashi daga nan zuwa karshen watan Yuni”, in ji shi. 

Borno: Ana Ci Gaba Da Tantance Ma’aikata

Yayin da ake aiwatar da biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga wasu ma’aikatan Jihar Borno, gwamnatin na gudanar da wani atisayen tantance ma’aikata na kwarai a kananan hukumomi.

A cewar kungiyar NUT reshen Jihar Borno, malamai a matakin jihad a kananan hukumomi na karbar mafi karancin albashi na Naira 70,000, sai dai sauran nau’o’in malaman da aka sanya wa horo na tsawon wata uku, daga nan ne za su fara karbar mafi karancin albashin.

Shugaban kungiyar ta NUT, Comrade Yusuf Inuwa, ya roki a kara wa kafatanin ma’aikatan da suka fito daga kananan hukumomi 27 na jihar, inda ya ce; har yanzu ma’aikatan kananan hukumomin ba su ci gajiyar karin mafi karancin albashin ba.

Yobe: Har Yanzu Ana Bin Tsohon Albashi

Wasu malaman makaranta a Jihar Yobe sun yi ikrarin cewa, ba a biya su mafi karancin albashi na Naira 30,000 da kuma wannan na Naira 70,000 ba. Har ila yau, sun dora alhakin hakan; kan shugabannin kananan hukumomi, wadanda suka dage kan cewa; ba za su iya biyan tsoffi da kuma sabon mafi karancin albashin ba, ba tare da korar wasu daga cikin malamai da ma’aikatan kananan hukumomi ba.

Don haka, shugabannin kungiyar NUT da ma’aikatan kananan hukumomi, sun yi kira ga Gwamna Mai Mala Buni, da ya tabbata ya aiwatar da biyan wannan mafi karancin albashi na Naira 70,000.  

Ogun: An Fara Biyan Mafi karancin Albashin Tun 2024

A Jihar Ogun, kungiyar hadin gwiwa (JNC) kan biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata ta tabbatar da cewa; Gwamnatin Gwamna Prince Dapo Abiodun, tun shekarar 2024 ta cika alkawarin da ta dauka na biyan sabon mafi karancin albashi.

kungiyar hadin gwiwar, wadda ta hada da NLC da TUC, ta bayyana cewa; ma’aikatan Jihar Ogun ba su da wata matsala da gwamnatin jihar, dangane da batun wannan sabon mafi karancin albashi, sai dai kawai batun da suka shafi jin dadi da walwalar ma’aikata da sauran makamantansu.  

Ribas: Naira 85,000 Ake Biya A Matsayin Mafi karancin Albashi

A Jihar Ribas, malaman makaratun firamare da na sakandiren gwamnati da kuma ma’aikatan kananan hukumomi, na karbar Naira 85,000 a matsayin mafi karancin albashin da gwamnan da aka dakatar, Sir Siminalayi Fubara ya amince ya biya.

Da yake tabbatar da hakan ga LEADERSHIP, shugaban kungiyar NUT Dakta Collins Echikpu ya ce; malamai a jihar sun fara karbar sabon mafi karancin albashin.

Filato: Ta Fara Biya Tun 2024

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) reshen Jihar Filato, Kwamared Yohana Makwin ya tabbatar da cewa; gwamnatin jihar ta fara aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi, tun a watan Disambar 2024. 

Makwin, ya shaida wa LEADERSHIP a Jos cewa; gwamnatin jihar na ci gaba da biyan sabon mafi karancin albashin. Haka nan, takwaransa Kwamared Kefas Nanpan, ya sake tabbatar da al’amarin.  

Katsina: Ita Ma Ta Bi Sahun Biyan Naira 70,000

A Jihar Katsina, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Nijeriya (NULGE), Kwamared Nasiru Wada Mai Adua, ya yaba wa Gwamna Umaru Dikko Radda, bisa jajircewarsa na kyautatawa ma’aikata

Ya yaba wa gwamnan, bisa aiwatar da biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 da kuma tabbatar da biyan kudaden giratuti na ma’aikatan da suka yi ritaya, tun daga watan Disambar 2024. Nasiru, ya bayyana hakan a matsayin sauki ga ma’aikata da kuma ‘yan fansho a jihar.

Kwara: Na Biyan Albashin Bai-daya

Ana biyan ma’akatan kananan hukumomi da malamai mafi karancin albashi na Naira 70,000 a Jihar Kwara.

Kakakin kungiyar kananan hukumomin Nijeriya (ALGON), sannan kuma Shugaban karamar Hukumar Ifelodun, Barista Femi Yusuf, ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa da LEADERSHIP a Ilorin.   

Ya bayyana cewa, Jihar Kwara; jiha c eta musamman wadda a koda-yaushe kananan hukumomi da jiha ke tafiya bai-daya, wajen aiwatar da tsarin jin dadin ma’aikata. Shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Murtala Olayinka, ya tabbatar da wannan batu na Kakakin kungiyar ta ALGON. 

Anambra: Na Biyan 82,000 A Matsayin Mafi karancin Albashin Ma’aikata

A Jihar Anambara, ma’aikatan kananan hukumomi na karbar Naira 82,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata. Dukkanninsu, shugaban kungiyar NLC Kwamared Humphrey Nwafor da kuma shugaban kungiyar NULGE, Kwamared Chudi Orakwe, sun tabbatar da biyan kudin a wata tattaunawa da suka yi da LEADERSHIP. 

Imo: Malamai Da Ma’aikatan kananan Hukumomi Sun Dara

Gwamnan Jihar Imo, Gwamna Hope Uzodimma; ya aiwatar da biyan Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata da malaman makaranta. Babban sakataren yada labaran gwamnan, Oguwuike Nwachuku ya ce; hakan ya yi daidai da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar. Da yake zantatawa da LEADERSHIP, shugaban kungiyar ta NULGE na jihar, Kwamared Charles Okere, ya yaba wa gwamnan; bisa aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashin na Naira 70,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi.   

Ondo: An Cika Alkawari

A Jihar Ondo, LEADERSHIP ta tattaro cewa; ana biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga kowane bangare na ma’aikata. Wani jami’in kungiyar NULGE day a nemi sakaye sunansa, ya bayyana cewa; gwamnan ya cika alkarin day a yi wa ma’aikata, dangane da mafi karancin albashi. 

Edo: Albashi Ya karu Zuwa Naira 75,000

A Jihar Ido, ma’aikata a halin yanzu na karbar Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, wadda tsohuwar gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki ta gabatar. A yayin bikin ranar Mayun 2025, Gwamna Monday Okpebholo ya kara albashin zuwa Naira 75,000 tare kuma da alkawarin ci gaba da inganta jin dadin ma’aikatan jihar. Sai dai, shugaban kungiyar malamai NUT na jihar, Bernard Ajobiewe ya ce; har yanzu ba a kamma shirye-shiryen fara biyan ba.

Akwa Ibom: Uniform Template

Shugaban kungiyar ma’aikata na jihar, Kwamared Sunny James, ya tabbatar da cewa; ma’aikatan kananan hukumomi, ba su fuskanci matsala kan batun mafi karancin albashin na Naira 70,000 ba. Ya alakanta batun samun daidaito na biyan ma’aikatan masana’antu da jihohi da kuma kananan hukumomi. Da yake jawabi a Uyo, ya kara da cewa; Gwamna Umo Eno, ya kara albashi zuwa Naira 82,000.

Kano: An Aiwatar Da Sabon Mafi karancin Albashi

Ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare na karbar Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi. Wata malama da ke mataki na 10 ta bayyana cewa, albashinta yanzu ya koma Naira 82,000. 

Ekiti: Ta Na Biyan Dukkannin Ma’aikata Naira 79,000 A Matsayin Mafi karancin Albashi

Ana biyan dukkanin ma’aikatan kananan hukumomi Naira 79,000. Shugaban NULGE na jihar, Kwamared Oluseyi Olatunde ya ce; an fara aiwatar da biyan tun a watan Junairun 2025.

Takwaransa na kungiyar NUT, Kwamared Adedeji Egbeyemi, ya tabbatar da hakan; inda ya bayyana cewa, an fara biyan ma’aikatan tun a shekarar da ta gabata.  

Delta: Ta Fara Biya Tun Shekarar 2024

An fara biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati, musamman malaman makaranta tun a watan Nuwamban 2024.

Sakataren kungiyar NUT na jihar, Kwamared Dan Basime, ya bayyana jin dadinsa da yadda aka gaggauta biyan. Kwaminan ilimin firamare, Dakta Kingsley Ashibogwu, ya bad a tabbacin ci gaba da biyan. A baya dai, Gwamna Sheriff Oborebwori, ya umarci dukkanin shugabannin kananan hukumomi 25 tare da kungiyoyin ALGON, NUT da kuma NULGE, da tabbata sun aiwatar da biyan sabon tsarin mafi karancin albashin.

Niger: Ta Aiwatar Da Fara Biyan Naira 80,000

Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya sanar da biyan Naira 80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi da kuma malaman makaranta.

Shugaban kungiyar NLC kuma babban jami’in kungiyar NULGE, Kwamared Idris Lafene, ya tabbatar da cewa; an fara aiwatar da biyan wannan sabon mafi karancin albashi ga dukkanin ma’aikatan gwamnati.

Enugu: An Fara Biyan Naira 80,000 

Gwamnatin Gwamna Peter Mbah, ta aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 80,000 ga dukkanin daukacin ma’aikatanta. Shugaban kungiyar NUT, Kwamared Theophilus Nweke, ya tabbatar da cewa; babu wani banbanci wajen aiwatar da fara biyan wannan sabon tsarin albashi.

Osun: Tana Biya Duk Da Rike ata Kudade Da Ake Yi

Duk da hana kudaden kananan hukumomi daga asusun tarayya, gwamnatin jihar ta ci gaba da biyan albashi.

Shugaban kungiyar NULGE na jihar, Dakta Bayo ya shaida wa LEADERSHIP cewa; takun-saka tsakanin shugabannin kansiloli, bai shafi batun biyan ma’aikata albashi ba. Dukkanin ma’aikata, na karbar sabon mafi karancin albashin Gwamnatin Ademola Adeleke na Naira 75,558.24 tun daga watan Junairun 2025. 

Amma, duk da fara biyan wannan mafi karancin albashi na 70,000, har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a fadin wannan kasa, sakamakon matsalar tsadar kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Wasu na ganin, ko da 100,000 aka fara biya a matsayin sabon mafi karancin albashi, mafi yawan kananan ma’aikata; ba za su iya daukar nauyin iyalansu yadda ya kamata, duba da yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare, komai ya yi tsada.

Sanin kowa ne, yanzu haka; wannan 70,000, ba za ta taba iya saya wa magidanci buhun shinkafa daya ba, ban da batun kula da harkar lafiya, cefane na yau da kullum, wutar lantarki, ruwan sha, sabulun wanka da wanki, kudaden zirga-zirga, biyan kudin makarantar yara da sauran dawainiya ta yau da kullum.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Matsin RayuwaNijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Rundunar PLA Ta Soki Birtaniya Bisa Zuzuta Abun Da Ya Wakana Yayin Da Jirgin Ruwan Sintirinta Ya Keta Ta Zirin Taiwan 

Next Post

Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje

Related

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

12 minutes ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

24 minutes ago
Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
Manyan Labarai

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

11 hours ago
Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi
Manyan Labarai

Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

12 hours ago
NNPP
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

1 day ago
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Manyan Labarai

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

1 day ago
Next Post
Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje

Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra'ila – Ministan Harkokin Waje

LABARAI MASU NASABA

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

September 19, 2025
Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

September 19, 2025
Nijeriya

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

September 19, 2025
Xi Jinping Ya Aika Wasikar Taya Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwar Jam’iyyar Zhigong Ta Sin

Xi Jinping Ya Aika Wasikar Taya Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwar Jam’iyyar Zhigong Ta Sin

September 19, 2025
An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki

An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki

September 19, 2025
Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

September 19, 2025
Nijeriya

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (2)

September 19, 2025
Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna 

Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna 

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.