Duk Da Yankan Albashi: Ma’aikata A Kano Sun Yaba Wa Gwamna Ganduje

Laifuka

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Duk da cewa a kan sami wadansu lokuta da ake yankar wani abu daga cikin albashin ma’aikatan Jihar Kano, amma sai gashi ma’aikatan suna yin godiya ga Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, saboda kokarin da yake yi wajen ganin ana biyan albashi duk karshen wata ba tare da tsaiko ba.

Sannan mafiya yawan ma’aikatan da suka sami zantawa da wakilinmu sun nunar da cewa, a wad­ansu jihohin ana daukar kwanaki bayan cikar wata kafin a biya albashi, yayin da wadansu jihohin ma’aikata suna bin albashin wata daya zuwa biyu kafin a biya su, domin haka a cewarsu, Gwamnatin Ganduje tana kokari sosai wajen biyan albashi.

Dangane da batun yankan kudade da aka samu kuwa, Malam Usman Abdullahi, ma’aikaci a Gwamnatin Jihar Kano ya ce, duk lokacin da aka sami gibin kuddaden gudanar da wadansu ayyu­ka ko kuma abin da ake da shi a hannu ba zai isa a biya kowa albashin sa daidai ba, za’a iya rar­rage kudaden ma’aikata ta yadda za’a sami nasarar biyan albashi maimakon daukar matakin korar ma’aikata.

Domin haka ne ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ma’aikatan Gwamnatin jJihar Kano da su kara juriya kan wannan lamari, na yan­kar wani abu daga cikin albashinsu wanda a cew­arsa maimakon rage ma’aikata gara ace albashin ake dan yanka domin ganin an biya kowa albash­insa duk karshen wata kamar irin wannan hikimar da Gwamna­tin Ganduje ke yi.

Sai dai dukkanin ma’aikatan Gwamnati da aka samu zantawa da su sun roki Gwamnatin Jihar ta Kano da ta bullo da wani shiri na rage kashe kudade a harkokin yau da kullum, domin ganin an sami kudaden da za a biya ma’aikatan da suka bar aiki domin tallafa wa rayuwarsu da ta iyalin su.

Exit mobile version