Kamar yadda shafin Adabi ke zakulo maku manyan marubuta littattafan Hausa har ma da kanana, domin jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rayuwarsu har ma da rubutunsu. Yau ma shafin na tafe da wata fasihiyar marubuciyar wadda ta shafe shekaru takwas a duniyar rubutu, NABEELA AMINU DIKKO. Wacce aka fi sani da NABEELA DIKKO, ta bayyana wa masu karatu irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta fara rubutu, tare da bayyana yadda take jin dadi idan ta ga mutane suna amfana da rubutunta tare da daukar darasi a kai. Akwai sauran batutuwa da dama da ta fada a kan rubutu da marubuta a tattaunawarta da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Ya sunan bakuwar?
Assalamu Alaikum, sunana Nabila Aminu Dikko wacce mafi yawan mutane, musamman a duniyar marubuta suka fi sani da Nabeela Dikko.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Bismillahir rahmanir rahim, kamar yadda na fada a baya sunana Nabeela Dikko, an haife ni a garin Argungun da ke cikin jihar Kebbi a shekarar 1994, nayi karatun addini har nayi nasarar sauke alkur’ani mai girma da sauran littattafan addini wanda har yanzu ina fafutukar neman sanin wasu daga cikin littafan. A bangaren boko kuma sai hamdallah nayi karatu daga matakin firamare har zuwa kwalejin ilimi wanda na kammala a shekarar 2018 inda na karanci Hausa/Islam, daga nan kuma nayi aure ina zaune tare da iyalina duk a jihar Kebbi.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutu?
Abubuwa da dama sun zaburar da ni a baya, da farko dai ni ma’abociyar yawan karatu ce, ina son karatu kuma rubutu tun a makaranta ba ya yi mini wuya, to na jima ina karatu har daga baya na rikida daga makaranciya na fara rubutu domin ina sha’awar isarwa ‘yan uwa makaranta abin da zai iya amfanar su, daga nan na fara koyo har dai na tsunduma a cikin rubutu.
Kamar wanne bangare kika fi maida hankali a kai wajen yin rubutu?
Hankalina ya fi karkata ga zamantakewa, domin abubuwan da ke wakana a wannan karni duk suna da nasaba da ita, to na fi zakulo matsalolin yau da kullum in tsara rubutu mai ma’ana wanda dubban mutane za su iya amfana da shi su kuma dauki darussa.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Duk wata nasara ba ta taba samuwa, sai an sha gwagwarmaya sosai, haka dai a hankali aka fara har komai ya daidaita.
Daga lokacin da ki ka fara kawo yanzu kin rubuta labari sun kai kamar guda nawa?
Dankari! Gaskiya ba zan iya cewa ga adadin labaran da na rubuta ba, musamman gajerun labarai ko kuma na gasa, amma dai a kalla na rubuta littafai goma sha biyar (15).
Wanne labari ne ya zamo bakandamiyarki cikin wadanda ki ka rubuta?
Ni duk littafaina Bakandamiya ne, amma dai kamar wanda na yi fice da su, su ne; Tarbiyya, Almajiranci ko Aikatau, Uwar ‘Yan Mata sai kuma Bodarar Amarya.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar masu kina sha’awar fara rubutu, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
To, gaskiya lokacin da na fara rubutu gidanmu ma ba su sani ba, domin ina karatu lokacin na san ma ba za a bari ba, shi ya sa na fara yi a boye, kwatsam sai ga gidan rediyon tarayya na Ekuity FM sun nemi fara karanta daya daga cikin littafina, to daga lokacin ne dai gidanmu da ‘yan uwa da abokan arziki suka san ina rubutu, kuma gaskiya abin ya yi musu dadi har suna alfahari da ni.
A cikin labaran da ki ka rubuta akwai wanda ki ka buga?
Akwai littafina mai suna UWAR ‘YAN MATA, wanda gwarazan BBC HIKAYATA na 2022 suka saka gasa a lokacin, cikin iyawar mai duka ina daga cikin wanda suka ci gasar sai suka dauki nauyin buga mini, sannan akwai KOWA YA CI BASHIN KURA shi ma yana dab da fitowa kasuwa In sha Allah.
Wanne labari ne cikin labaran da kika rubuta ya fi ba ki wahala?
A duk lokacin da marubuci zai daura damarar rubutu, dole ne sai ya zurfafa tunaninsa da kuma bincike, to a gani na duk wani rubutu mai inganci wanda ake so ya zama ingantacce a wurin mutane sai an sha wahala kafin a rubuta shi.
Kamar da wanne lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?
Rubutu zuwa ne yake yi, a duk lokacin da na ke jin son yin rubutu ina yi, amma mafi yawa nafi yi da yamma ko kuma da dare.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu?
Kalubale kam ba za a rasa ba, domin harshe da hakori ma sukan samu sabani, ballantana mutane masu abin mamaki, ana samun kalubale a wurin mutane amma duk abin da ka mayar banza to ba za ya taba damun ka ba, don haka ni kam ba na fuskantar kowanne kalubale a yanzu.
Wadanne irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Nasarori Alhamdulillah a koda yaushe ina fada kuma zan kara fada, arzikin mutane ma nasara ce babba, Allah ya ba mu arzikin soyayyar mutane na ciki da wajen najeriya, ko’ina ana girmama ni wannan nasarar abin bugun gaba ayi tinkaho ce, sannan an samu nasarori da dama ta fannin rubuta kamar gasa da dai sauran su sai hamdalla.
Ya kika dauki rubutu a wajenki?
Rubutu a wurina abu ne mai girma da daraja, domin wata hanya ce ta isar da sako kai tsaye ga mai karatu sannan wa’azantarwa ne, ilimantarwa ne.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Ina da burika da dama a kan rubutu, domin rubutu shi ne ya zabe ni sannan ya ba ni damar kaunar shi fiye da tunanin mizanin masarrafar tunanina, fatana rubutuna ya zagaya ko’ina a duniya in yi fice in kuma shiga jerin manyan marubutan duniya.
Mene ne ya fi saurin sa ka ki farin ciki game da rubutu?
Idan na tuna mutane da dama na amfana da abubuwa ta silar rubutuna, sannan kuma suna fahimtar kurakurensu har su gyara idan sun karanta littafaina, wani zubin har suna godiya tare da yi mini addu’a da fatan alheri ni da ahalina, wannan abun yana matukar tasiri a raina ina kuma jin dadi.
Bayan rubutu da ki ke yi kina yin wata sana’ar ne?
Eh! ba za a rasa sana’oi ba haka na online, ina yi kamar saye da sayarwa.
Ta yaya kike iya hada aikin gida da kasuwanci da kuma rubutunki?
Komai a rayuwata yana da lokacinsa, kafin na yi abu sai na fara sanin wanne lokaci zan yi shi, ina da lokacin da nake warewa domin gudanar da ayyukana na yau da kullum.
Me za ki ce da masoyanki?
Ina miko musu gingimemiyar gaisuwa, sannan su sani a duk inda suke ina kaunar su, sannan ina alfaharin samunsu a matsayin masoyana domin tafiyata ba za ta taba yi ba sai da su, na gode sosai Allah ya bar zumunci Amin.
Ko kina da wadanda za ki gaisar da su?
Ina gaida kawata Rabi’a Sidi Bala (Leadership), ina gaishe ki Princess Fatyma Zarah, ina mika sakon gaisuwata ga ‘yan uwana da abokan arziki tare da marubuta a duk inda suke Allah ya sada mu da alheransa Amin.
Muna godiya, ki huta lafiya.
Ni ma na gode, Allah ya kara daukaka jaridar LEADERSHIP Hausa.