Yayin da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO), ta sanar da sanya ginin da ya raba birnin Beijing da hamadar Badain Jaran da yankin kiyaye tsuntsaye masu kaura, wanda ke kusa da gabar rawayen teku da tekun Bohai na kasar Sin, cikin jerin kayayyakin gargajiya na duniya da aka yi gado, shugaban kasar Xi Jinping, ya bukaci a kara kokarin kare al’adu da abubuwa masu daraja.
Al’adun gargajiya su ne asali da madubin dubawa ga duk wata al’umma, kuma duk wata al’umma da ta rasa al’adunta, duk ci gaban da za ta samu, to ta rasa asalinta. Shi ya sa Hausawa kan ce, “duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi.”
- Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam
- Xi Ya Nanata Bukatar Kare Al’adu Da Kayayyakin Gargajiya Na Sin
A lokacin da na dauka ina zaune a kasar Sin, na lura cewa, gwamnatin da al’ummar Sinawa na daukar al’adunsu da tarihi da kayayyaki da wuraren gargajiya da muhimmancin gaske. Haka kuma, wani abu da kan burge ni shi ne, ban taba haduwa da wani Basinen da bai san asalinsa ko tarihi ko al’adun kasarsa ba.
Duk da cewa kasar Sin ta bude kofarta ga duniya, kuma ana kara samun cudanya tsakanin al’ummarta da na kasashen ketare, ko kadan bai sanya sun yi watsi da al’adunsu ko sun ari na wasu ba, har kullum, su kan yi abubuwa ne da suka dace da al’adunsu da yanayin kasarsu.
A wannan gaba da kasar Sin ta dukufa kan zamanintar da kanta, a daya bangaren, tana dukufa wajen karewa da kara yayata al’adunta, domin samun fahimta da jituwa tsakaninta da sauran al’ummomin duniya.
Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, sanya wadannan kayayyaki cikin jerin na UNESCO na da muhimmanci ga aikin zamanintar da kasar Sin. Wato yayin da ake zamanintar da kasar Sin, ba za a bar batun raya al’adun a baya ba, kuma wannan a ganina, na daya daga cikin dalilan da suka sa kasar ke samun ci gaba da zaman lafiya tsakanin al’ummominta da kuma darsuwar kishin kasa a zukatan su.( Fa’iza Mustapha)