Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodoke, ya bayyana takaicinsa kan wuyar da mambobin kungiyar za su fuskanta wajen komawa jami’o’insu a ranar Litinin saboda basu da kudin mota.
Farfesa Emmanuel ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels dangane da janye yajin aikin na ASUU a ckin wani shiri mai suna Sunday Politics. BBC Hausa ta rahoto.
Farfesa Emmanuel ya ce a shekarun baya malaman Jami’a na zaune ne a gidajen da aka tanadar musu kusa da makaranta, amma a yanzu ba haka lamarin yake ba. yawancin Jami’o’i basa iya samarwa Malaman wuraren zama.
Ya ce, Mambobin kungiyar za su fuskanci wahalhalu da dama, musamman wajen biyan kudin motar komawa aiki domin koyar da dalibai saboda ba a biya su albashinsu ba har na tsawon wata takwas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp