An dage karawar da Bayern Munich za ta yi da Union Berlin saboda dusar kankara a babban birnin Munich kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Asabar.
An shirya gudanar da wasan ne a ranar Asabar da yamma amma sanarwar manema labarai daga Bayern ta ce hatsarin tsaro da yanayin zirga-zirga ya sanya aka dage wasan.
- Na Fi Jin Dadin Rubutu Da Sassafe Ko Dare – Princess Mazadu
- Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana
Karancin yanayin zafi ya haifar da dusar kankara a kudancin Jamus, musamman a Munich.
Gabanin soke wasan dai tuni hukumomin sufuri na birnin Munich suka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin mafi girma na Munich, yayin da cunkoson ababen hawa suka tsaya cak.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Bayern ta ce akwai hatsari mara misaltuwa ga ‘yan kallo kuma ta bayyana cewa akwai wahalar isa filin wasa na Arena.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Jamus (DFL) da ke gudanar da gasar Bundesliga ta tabbatar da soke gasar a ranar Asabar kuma ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sabuwar ranar da za a buga wasan.