Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’nnuti (EFCC) ta kama wani dan takara a kujerar majalisar dokokin jihar Kogi a karkashin jam’iyyar NNPP, Ismaila Yusuf Atumeyi da tsabar kudi har Naira miliyan 326 da kuma dala 140,500.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce Atumeyi, wanda ke neman wakiltar mazabar Ankpa II a majalisar dokokin jihar Kogi, an kama shi ne a ranar Lahadi, 30 ga Oktoba, 2022 tare da wani Joshua Dominic, wanda ake zargin dan damfara ne a wani samame da hukumar ta kai a Masedonia Street, Queens Estate, Karsana, Gwarinpa a Abuja.
Hukumar EFCC ta ce, kama wadanda ake zargin ya biyo bayan bin diddigin wasu ‘yan damfarar yanar gizo da suka kutsa cikin wani banki, inda suka karkatar da makudan kudade har Naira Biliyan N1.4.
‘Yan damfarar sun tura Naira miliyan 887 cikin asusun Fav Oil and Gas Limited, inda daga nan aka tura wa ‘yan canji kudade da wasu dillalan motoci domin sayen motocin alfarma.
Haka kuma an kama wani tsohon ma’aikacin bankin, Abdumalik Salau Femi, wanda ake zargin ya bayar da bayanan sirrin bankin wanda ya kai ga nasarar karkatar da makudan kudaden.