Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta gurfanar da Farfesa Uche Chigozie Edwin a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas, bisa zargin damfarar biliyan N1.4.
An gurfanar da Edwin tare da wasu kamfanoninsa biyu.
- Wakilin Sin Ya Bayyana Rashin Gamsuwa Da Yadda Amurka Ta Gabatar Da Daftarin Kudurin Kwamitin Sulhu Kan Sudan Ta Kudu
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Cire Tallafin Man Fetur Kafin 29 Ga Watan Mayu
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da hukumar ta fitar ta shafin Twitter a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, Edwin ya gurfana a gaban kotu kan tuhume-tuhume 11 da suka hada da hada baki, rikewa da kuma musayar kudade.
Sanarwar ta ce: “Hukumar EFCC ta shiyyar Legas, a ranar 16 ga watan Maris, 2023, ta gurfanar da wani Farfesa Uche Chigozie Edwin a gaban kotu bisa zarginsa da laifin zambar biliyan N1.4 a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke zaune a Ikoyi, Legas.
“An gurfanar da Edwin ne tare da kamfanonin sa, Visionary Integrated Consulting Limited, NEMAD Associates Limited da Revamp Global Enterprise a kan tuhume-tuhume 11 da suka hada da hada baki, rikewa da canja kudaden zuwa N1,473,367,046.04.”