Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen jihar Gombe ta gurfanar da Shugaba kuma Manajan Darakta na MB Lugga Global Travels and Tours Limited, Mustapha Mohammed, bisa zargin damfarar Naira miliyan 144 ta hanyar yin karya da kwace kuɗi da gangan.
An gurfanar da Mohammed ne a gaban mai Shari’a T.G. Ringim na babbar Kotun tarayya da ke Gombe, bisa zargin karɓar wannan adadin daga Hamza Ibrahim Maina da Ibrahim Arabia don shirya tafiyar Umrah a lokacin Azumin Ramadana na 2024.
A tuhuma ta farko, an zargi Mohammed da haɗa kai da wani Nazifi Sale Idris (wanda har yanzu ba a kama ba) don karɓar N97,080,000 daga Hamza Ibrahim Maina ta asusun bankinsa na Access Bank domin siyan tikitin jirgi, biza da masauki don tafiya Umrah, amma bai cika alƙawarin ba. Wannan ya karya dokar sashi na 1(1)(a) na dokar hana damfara ta 2006.
Lauyan EFCC, S. H. Sa’ad, ya nemi a sanya rana don fara shari’a tare da ajiye wanda ake zargi a gidan gyaran hali na Gombe. Amma lauyan wanda ake tuhuma, M.Z. Gambo, ya nemi belinsa, wanda lauyan gwamnati ya ƙi amincewa da hakan.
Mai Shari’a Ringim ya ɗage sauraron shari’ar don yanke hukunci kan buƙatar beli, tare da umartar a ci gaba da tsare Mohammed a gidan gyaran hali na Gombe.