Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta tuhumi tsohon babban lauyan Jihar Legas kuma Kwamishinan Shari’a, Supo Shasore (SAN), da laifin karkatar da kudade.
EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda hudu a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas a kan wanda ya kafa kamfanin Africa Law Practice NG & Co.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Aure ‘Ya’yan Tsohon Akanta-Janar Na Zamfara Da Suka Sace
- An Cafke Mutane 16 Da Ake Zargi Da Satar Mai A Ribas
Ana zargin Shasore mai shekaru 58 da jawo wani Olufolakemi Adelore ya karbi tsabar kudi Dala 100,000 ba tare da bin hanyar da ta dace ba.
An yi zargin biyan Misis Adelore ne ta hannun wasu mutane biyu, Auwalu Habu da Wole Aboderin.
Tsohon Atoni-Janar din an yi zargin ya biya wani Ikechukwu Oguine tsabar kudi Dala 100,000 ba tare da ya bin ta hannun ma’aikatar kudi ba.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce an aikata laifin ne a ranar 18 ga Nuwamba, 2014 ko kuma a ranar 18 ga watan Nuwamba.
Laifin ya ci karo da sashe na 78 (c), 1 (a) da 16 (1) (d) da 18 (c) na dokar haramtattun kudi na 2011 kuma ana sa ran hukunta su karkashin sashe na 16 (6) da 16. (2) (b) na wannan Dokar.
Mai shari’a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya ya sanya ranar 20 ga Oktoba, 2022 domin gurfanar da Shasore.
Adelore da Oguine sun kasance lauyoyin ma’aikatar albarkatun man fetur da kuma kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC).
A shekarar 2012, kamfanin ya samu kyautar Dalar Amurka biliyan 9.6 a kan gwamnatin tarayya kan wata kwangila.
Shasore, wanda ya wakilci Nijeriya, ana zarginsa da raunana karfin tsaron kasar a kan kamfanin British Virgin Island.
Hukumomin kasar sun ce ya yi aiki ta hanyar da ba ta dace ba, ta hanyar aikata cin hanci da rashawa da kuma gaza yi wa marigayi Michael Quinn, wanda ya kafa P&ID tambayoyi.
Har ila yau, Shasore ya gaza mika muhimman takardu ga Bolaji Ayorinde, Babban lauyan da ya maye gurbinsa a shari’ar.