Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), reshen Kano ta kama ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano guda 25 da ake zargi da aikata damfara a Intanet.
An kama su ne a ranar Litinin, 21 ga watan Yuli, 2025, a wani samame da jami’an hukumar suka kai kusa da Jami’ar BUK.
- Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
- Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
EFCC ta sanar da hakan ne a shafinta na X a ranar Laraba.
Hukumar ta bayyana cewa duk waɗanda aka kama ɗalibai ne a jami’ar, kuma an kama su ne bayan samun sahihan bayanai da ke nuna cewa suna da hannu da aikata damfara a Intanet.
EFCC ta ce ta bi diddigin waɗanda ake zargin na tsawon makonni kafin kama su, inda aka gano suna aikata damfara ta Intanet, satar bayanan mutane, da kuma dabarar karɓar kuɗi ta hanyar zamba.
Kayan da aka gano a wajen samamen sun haɗa da wayoyin salula da dama, kwamfutoci, na’urorin haɗa Intanet da mota ƙirar Honda Accord.
Sunayen waɗanda aka kama sun haɗa da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan da Abubakar Abusufyan.
Sauran sun haɗa da Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, Issac Dosunu, Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman da Dauda Abdulhamid.
EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp