Hukumar EFCC ta kama wani matashi mai suna Muhammad Kabir Sa’ad a Jihar Kaduna bisa zargin wulaƙanta takardun Naira a kafafen sada zumunta.
EFCC ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin.
- Aikin Hajjin 2025 Ya Fara A Hukumance Yayin Da Tawagar NAHCON Ta Musamman Ta Tashi Zuwa Makkah
- An Kammala Horon Hadin Gwiwa Tsakanin Sojojin Saman Sin Da Masar Cikin Nasara
Ta ce matashin ya wallafa bidiyo a TikTok da Instagram yana watsar da kuɗi a ƙasa tare da tattaka su.
A cikin bidiyon, matashin har ya ƙalubalanci hukumar da cewa “idan za ku iya ku zo ku kama ni”, wanda hakan ya janyo hankalin jami’an EFCC.
Bayan gudanar da bincike, jami’an hukumar daga ofishin Kaduna sun kama shi a unguwar Tudun Wada, inda yanzu haka yana hannunsu don ci gaba da yi masa tambayoyi.
EFCC ta ce za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp