Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar APC ya koma Social Democratic Party (SDP), domin cika burinsa na kawo sauyi a siyasar Nijeriya.
A cewar El-Rufai, ya miƙa takardar ficewarsa daga APC ga mazaɓarsa a Kaduna ranar Litinin.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]
- Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto
Ya ce bayan tuntuɓar jagororinsa da magoya bayansa, ya yanke shawarar komawa SDP domin ci gaba da fafutukarsa a siyasa.
Alƙawuran Da El-Rufai Ya Ɗauka
El-Rufai ya bayyana cewa a matsayinsa na mamba a jam’iyyar SDP, zai yi aiki tare da sauran ‘yan siyasa domin:
- Haɗa kan abokan hamayya: Ya ce zai haɗa kai da jagororin siyasa domin kafa gagarumae tafiyar adawa da za ta ƙalubalanci APC a zaɓe.
- Kawo sauyi a Nijeriya: Ya ce yana da burin ganin an samar da ci gaba ta hanyar manufofi masu amfani ga al’umma.
- Ƙarfafa guiwar matasa: Ya yi alƙawarin kawo sauyi a tsarin siyasa domin matasa su samu dama su taka rawa a shugabanci.
Dalilan Barinsa APC
El-Rufai ya bayyana cewa matsaloli da rikice-rikicen cikin gida sun hana APC tafiya bisa turbar da aka kafa ta a 2013.
Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba.
Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp