‘Yan Afrika suna wani magana da suke cewa, ‘Sauro ba shi da wani abun nunawa’, amma yana da muryar rera wake-wake. Tonon sililin abun kunya ya fara ne daga wurin Honourable Muhammad Gudaji Kazaure wanda a hankali lamarin ya zama babba da ka iya bata gwamnatin Buhari.
Mutane da yawa suna tunanin cewa don dan majalisan ya yi tonon sililin ne saboda zai koma zauren majalisa ba. Haka kuwa wasu sun gano abubuwa daga bayanansa. Wadanda suka bi labarin da zuciya daya za su sami alamun gaskiya a cikin bayanan a lokacin da yake gabatar da shaidun cewa shugaba Buhari ya nada shi ya yi aiki a matsayin sakataren kwamitin don gano dukkanin kudaden da ake karba a matsayin ‘stamp duty’ daga bankuna.
Abun lura da ban mamaki shi ne a lokacin da Garba Shehu ya zama mai magana da yawun Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fito fili yake karyata bayanan Gudaji. Wadanda suke ganin girman abun sun yi tunanin bayan wannan rahoton, babban kotun tarayya za ta ayyana cewa jami’an DSS su kama Gwamanan CBN, Godwin Emefiele.
Ana zargin gwamnan CBN da aikata muyagun laifuka. Duk da yake ba wannan ne lokaci na farko da wannan gwamnati ta yi abun kunya ba kan abubuwa masu kama da wasan kwaikwayo. ‘Yan kasa sun shaida abun da ya faru da Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari da Dan’uwan Buhari, Mamman Daura. Akwai kuma wani abu da ya faru tsakanin tsohon shugaban DSS, Lawal Daura da tsohon shugaban EFCC, Magu. Sai kuma tsakanin tsofaffin shugabannin sojoji, Lt Janar Buratai da Air Marshall Abubakar. Yanzu kuma Emefiele da Bichi. Abubuwan ban mamaki dai ba sa karewa a wannan gwamnati.
Masu nazarin lamuran yau da kullum sun bayyana cewa abubuwan kunyar da ake a wannan gwamnati suna sanyawa a mantawa da abubuwan da suka shafi kasa, musamman tsaro. Wadansu kananan abubuwan suna sanyawa a manta da muhimman abubuwa da suke da muhimmanci ga kasa. Can sai na tuna matsalar Okupe. A wasu wuraren ma ana kawo wasu abubuwa ne da suke dauke hankalin ‘yan kasa kamar na macizai ko birrai ko gara.
A lokutan siyasa, kamar wannan wani zai yi mamakin yadda wannan abun zai faru. Fallasar da Gudaji ya yi a karbe shi da idon basira. A maimakon haka sai a mayar da hankali kan tsaro da siyasar kasa. Akwai abubuwa guda uku da ya kamata a hassaso a cikin wannan abun kunyar.
Na farko, bayanan Gudaji a kan shugaban kasa wanda mai magana da yawunsa yake musantawa wanda ya tabbatar da cewa Buhari yana rauni makuka, musamman a bangaren yaki da rashawa. Ya ce muddin Buhari ya amince da mutum yakan bar shi da Allah kawai ko da ya same shi da wata matsala. Hakan ya saba da tunanin mutane da suka zabi Buhari a 2015. Tabbas da mutane ba za su zabi Buhari ba, da sun san haka yanayin shugabancinsa yake.
Na biyu, wannan fallasar ya tabbatar da cewa gwamnatin Buhari tana da abubuwa sosai da suke da alamomin tambaya wadanda su suka haifar da matsalar tattalin arziki da na tsaro. Tsohon Ministan sufuri, Amaechi ya yi bayanin rashin isassun kudade ne a bangaren tsaro ya haifar da harin da aka kai wa jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna. Haka kuma ya bayyana cewa shugaban kasa da ministan mai su suke da alhakkin hana satar mai da kuma bin diddigin kudade kamfanin NNPC. Kudaden kamfanin NNPC yana da matukar muhimmanci ga kudaden shiga na kasa musamman a lokacin da farashin mai ya tashi a duniya.
Dalili na uku, akwai bukatuwar a rika bin diddigin ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Tsarin da ake yi a yanzu shi ya haifar da matsalolin da aka ciki.
Idan muka tuna a baya, a lokacin Sanusi Lamido ya zargi cewa kamfanin NNPC bai sanya wa asusun gwamnatin tarayya ko sisi ba, sai gwamnati a wancan lokaci ta nada kwimiti na musamman don gudanar da bincike a kamfanin. A yanzu haka Gwamnan CBN ya bayar da rahoton cewa NNPC bai zuba ko sisi ba a asusun gwamnatin tarayya a gaba dayan shekarar 2022. Shugaba Buhari da shugaban kamfanin na NNPC sun tabbatar da hakan. Ana ta mamakin me ya sa gwamnatin Buhari ba ta gudanar da abubuwa masu kyau ne.
Duk da fallasa badakkalar Emefiele wanda yake da alamomin tambaya masu karfi a kansa. Shi ne kuma mutumin da ya karya dokar CBN na tsaya wa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyya mai mulki.
Tsarinsa na canjin kudaden waje yanayi ne na rashawa. Kwanan nan Emefiele ya ce kwamitin bankuna sun tara kudi da nufin gyara ‘National Arts Theatre’ daga Dala miliyan 100 zuwa Dala miliyan 200. Ko da Gudaji ya tabbatar da cewa Emefiele zai iya mayar da mutum biloniya cikin dare daya.
Kiraye-kirayen da ake yi game da bin diddigi ga alamu yana fada wa kunnuwan kurame ne don gwamnati ta sanya shinge tsakaninsu da ministoci da manyan jami’an gwamnati wadanda suke da zimmar gyara.
Al’umma su sani cewa sassa kamar DSS da NNPC da CBN da wasu sassa suna karkashin ma’aikatun tsaro wajen ba su kudade ne.
Tsayawa cewa wakilan wannan gwamnatin don bin diddigi za a gane cewa wannan gwamnati ta Buhari ta gaza wajen yaki da rashawa da samar da tsaro da inganta tattalin arziki.
A batun gaskiya makonni 23 da ya rage wa gwamnati ya yi kadan, amma akalla kasar za ta iya amfana a nan gaba.
Fallasar Gudaji na wasu adadin kudade daidai da abun da tubabben sarki ya yi a shekarar 2013. Amma a ko da yaushe mu rika tunawa da cewa duk wanda yake tunanin sauro ya yi kadan ya kawo wasu canji, bai yi tsawon dare ba ne da shi.