Emefiele: Juya Akalar Babban Banki Ga Ci Gaban Jama’a

Emefiele

Daga Kelvin Gilbert

“Burina a matsayina na Gwamnan Babban Bankin Nijeriya shi ne na tabbatar da cewa babban bankin ya fi mayar da hankali ga ci gaban mutane, saboda manufofi da shirye -shiryen sa za su karkata wajen tallafa wa ayyukan samar da ayyukan yi, da inganta hanyoyin samun bashi don bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu, (MSMEs), zurfafa shirin tallafi a fannin aikin gona tare da gina ingantaccen tsarin biyan kudi wanda zai taimaka wa fitarwa da shigarwa. ”

Wadannan su ne kalaman Mista Godwin Emefiele, a taron manema labarai na a ranar 5 ga Yuni 2014 bayan an nada shi Gwamnan Babban Bankin Nijeriya. Ya kuma yi alkawarin jagorantar babban bankin da ke kara kuzarinsa wajen gina tsarin kudi mai juriya wanda zai iya biyan bukatunci gaban Nijeriya.

A karshen wa’adin mulkinsa na farko na shekaru biyar a shekarar 2019, ‘yan Nijeriya da yawa za su iya ba da shaida cewa ba wai kawai ya cika wannan hangen nesan nasa ba ne, amma a zahiri ya tattala babban bankin wanda har zuwa yanzu ana ganin wani abu ne da ya yi nisa da mutane da rashin sanin halin da ake ciki a kan dan talaka. Ya saukar da matakin bankin zuwa matakin mutumin da ke kan titi. Ko talaka manomin karkara yanzu yana magana kan yadda CBN ya yi tasiri a nomansa.

Ya kirkiro dabarun kirkire -kirkire don bunkasa tushen albarkatun tattalin arzikin Nijeriya, don haka, samar da dubban ayyukan yi a harkar noma da kiyaye musayar kudaden waje suka yalwanta.

A lokacin da Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya a watan Yunin 2014, Nijeriya ta fuskanci kalubale da yawa da kuma tashe -tashen hankula daga tattalin arzikin duniya.

Ko yaya, tare da dabaru daga kungiyar kwararrun ma’aikata a Bankin, CBN ya sami damar daidaita tattalin arzikin tare da manufofin ci gaban mutane.

Kwararren masanin tattalin arziki mai kishin kasa, Emefiele, a jagorancinsa a CBN ya ba da himma ga kokarin inganta tattalin arzikin Nijeriya, daga dogaro da danyen mai da sauran abubuwan da ake shigowa da su zuwa abubuwan da za a iya samarwa a cikin kasar.

Duk da zazzafar suka daga masu ruwa da tsaki a gida da waje, Emefiele ya ci gaba da daukar matakan rage yawan makudan kudaden da kasar ke kashewa wajen shigo da kayayyaki kamar kifi da shinkafa, wanda ya kai Naira tiriliyan 1.3 a shekara. Dakushe aiwatar da manufar Bankin na takaita samun damar shigo da kaya Nijeriya zuwa abin da ke yanzu jerin abubuwa 43 da aka hana su canjin kudin waje, babu shakka ya haifar da gagarumin ci gaba a cikin samar da wadancan abubuwan a cikin gida da rage kudin shigo da kaya na Nijeriya.

Daga matsakaicin kusan dala biliyan 5.5, lissafin shigo da kayan masarufi na wata -wata ya ragu zuwa dala biliyan 2.1 a shekarar 2016 da dala biliyan 1.9 zuwa rabin shekarar 2017 zuwa kasa da dala biliyan 1 a shekarar 2018, ta hakan yana sauya yanayin da ake shigowa da shi daga kasashen waje.

A matsayin wani bangare na ayyukan ci gaba, CBN, karkashin Emefiele, tun 2014, ya kuma kafa Kwamitin Bankunan, da bullo da wasu shirye-shirye daban-daban duk da nufin samar da arziki da sanya manyan manufofi don samar da ayyukan yi ga yawan matasa a kasar.

Babban abin da Emefiele ya kirkiro a CBN shine tallafin ci gaba.

Ya yi imanin cewa Babban Bankin na CBN zai yi aiki a matsayin mai hada -hadar kudi ta hanyar bangarorin dabarun da za su iya samar da ayyukan yi da yawa.

Ya bayyana cewa CBN zai bunkasa shirye -shiryen ci gaba don kirkirar yanayi mai ba da dama tare da abubuwan da suka dace don karfafa kwararrun ‘yan kasuwa don habaka harkokinsu.

Kimanin watanni takwas bayan an sake nada shi a wa’adi na biyu, tattalin arzikin ya sake fuskantar koma -baya. A wannan karon, COBID-19 (Korona) wanda ta shigo cikin kasar a cikin 2020 ta haifar da rudani.

Barkewar cutar ta haifar da raguwar farashin danyen mai kuma sau daya ya fallasa raunin tattalin arzikin kasa. Danyen mai yana wakiltar kusan kashi 95 na kudaden shigar da Nijeriya ke fitarwa zuwa waje kuma koma-bayan da ake samu a kasuwar kayan yau da kullun yana da tasiri a tattalin arziki.

Barkewar cutar wacce ta fara a matsayin matsalar lafiya, ta rikide zuwa matsalar tattalin arziki kuma ta bukaci samo da wasu dabaru daga hukumomin kasafin kudi da na kudi a duk fadin duniya, gami da Nijeriya.

A Nijeriya, daidai da matakin farko na fuskantar lamarin, babban bankin da Emefiele ke jagoranta ya yi aiki cikin hanzari kusan a lokacin da cutar ta barke a cikin kasa, ta hanyar bayyana wasu matakai don daidaita tasirin kwayar cutar kan gidaje, kasuwanci da a matsayin tattalin arziki.

Emefiele ya ba da sanarwar tsawaita wa’adin shirye -shiryen tallafin bakin bankin, rage kudin ruwa, kirkirar cibiyoyin ba da bashi na naira biliyan 100; da Naira biliyan 100 ga cibiyoyin kula da kiwon lafiya, da Naira tiriliyan 1 ga masana’antu. Wasu sauran matakan sun hada da karfafa manufofin Babban Bankin bisa doka.

Watakila, mafi kyawun zamanin Emefiele shi ne abubuwan da ya yi a fannin aikin gona. A nan ya nuna fahimta da imani cewa Nijeriya tana da iyawa da ikon jagorantar duniya.

A yau, an bayyana Emefiele a matsayin babban aminin manoma a Nijeriya. Ya yi iyakacin kokarinsa don ganin ya dawo da martabar Nijeriya da ta bace a harkar noma, ya biya bukatun cikin gida da dakatar da fitar da ayyukan yi zuwa wasu kasashe sakamakon cutar da manoma da masana’antu na cikin gida.

Baya ga kiyaye canjin, da gabatar da manufar da ta hana shigo da kayayyaki 43 da canjin kudin waje na gwamnati da Emefiele ya yi, an samu inganta noman su da samar da su a cikin gida.

Sabbin manufofin da ya bullo da su kamar shirin Anchor Borrowers ‘Programme (ABP) da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Nuwamban 2015 ya haifar da juyin-juya hali a harkar daga darajar amfanin gona, musamman shinkafa da masara. Wannan sabon shirin na sa tallafin kudi ya tabbatar da cewa Nijeriya ta fito daga cikin masu shigo da shinkafa zuwa manyan masu samarwa, ta samar da manyan kasuwanni a kasashen makwabta. A yau, kasar na samar da tan miliyan tara na shinkafa a kowace shekara, wanda ta isa kasar har ma ta fitar da ita.

Kididdiga ta nuna cewa shirin ya zuwa yanzu ya samar wa da manoma miliyan 3.1 zuwa sama da naira biliyan 492 don noman hekta 3,801,397 a cikin kayayyaki 21 ta hannun cibiyoyin hada -hadar kudi 23 a cikin jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja.

Dangane da samar da ayyukan yi, shirin ya samar da ayyuka sama da miliyan uku kai-tsaye sakamakon daga darajar aikin gona.

A wani yunkuri na karfafa masana’antun cikin gida don samo albarkatun kasa, CBN, a karkashin Emefiele, ya takaita samun canjin kudin waje akan abubuwa 43. Hudu daga cikin wadannan abubuwan kadai, a lokacin, sun kasance suna cin sama da Naira tiriliyan daya na lissafin shigo da kaya Nijeriya na shekara-shekara.

Baya ga wannan, Bankin ya kuma samar da wata kafa ta masu saka hannun jari da masu fitar da kaya (I&E), wanda ya bai wa masu saka hannun jari da masu fitar da kaya damar saye da siyar da kudaden musaya a cikin farashin kasuwa.

Sauran manufofin da CBN ya bullo da su a karkashin Emefiele don karfafa wa mutane da kuma habaka tattalin arziki sun hada da, Shirin Ci gaban Kasuwancin Matasa (YEDP), Shirin Ci gaban Aikin Gona (AADS), Shirin Bunkasa Aikin Gona da Masu Kanana da Matsakaitan Masana’antu (AGSMEIS), da rijistar Jingina ta Kasa (NCR) da kaddamar da Tallafin Masana’antu (CIFI), wanda hadin gwiwa ne tsakanin CBN da Kwamitin Bankunan.

A bayyane yake cewa babu wata manufar CBN da ta shafi rayuwar talakawan Nijeriya kamar wadanda shugabancin Emefiele ya fara aiwatarwa. Lallai Emefiele ya rubuta sunansa da zinare a matsayin gwamnan babban bankin da mutane suka mayar da hankali a kai.

 

Gilbert masanin tattalin arziki ne da ke Abuja

Exit mobile version