Sabon kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya sake gayyatar Ahmed Musa, kyaftin ɗin tawagar, domin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su yi da ƙasashen Rwanda da Zimbabwe.
Wannan ne karo na farko da Ahmed Musa ke samun gayyata cikin tawagar bayan dogon lokaci ba tare da ya buga mata wasa ba.
- Natasha Da Akpabio: Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisar Dattawa Ƙorafinta
- A Otal Ya Mutu Ba ‘Yan Fashi Ne Suka Kashe Tsohon Kwanturolan NIS Ba – ‘Yansanda
Daga cikin ƴan wasa 35 da aka gayyata, akwai huɗu da ke taka leda a Najeriya, ciki har da Ahmed Musa daga Kano Pillars, Papa Daniel Mustapha na Niger Tornadoes, Koyode Bankole mai tsaron ragar Remo Stars, da Emmanuel Onyebuchi na Enugu Rangers.
A ranar 21 ga watan Maris, Super Eagles za ta tafi Kigali don buga wasa da Rwanda, sannan a ranar 25 za ta karɓi baƙuncin Zimbabwe a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.
A halin yanzu, Nijeriya na matsayi na biyar da maki uku a rukunin C, don haka tana buƙatar samun nasara a wasannin da ke tafe domin samun gurbi a gasar cin kofin duniya da za a buga a baɗi.