A cikin ‘Yan kwanakin nan al’ummar Jihar Kano musamman kwaryar birni na fama da matsalar faɗace faɗacen daba wanda a halin yanzu ke zama wata barazana ga zaman lafiyar jama’a.
A wannan karon lamarin na ɗaukar wani sabon salon ta yadda lamarin ya wuce tsakanin waɗanda ke faɗa da juna, a wasu lokutan tsakanin waccan unguwa da wancan, yanzu maharan sun fara kai irin wannan farmakin har cikin gidajen al’umma.
Wannan annoba ta faɗace faɗaɓen da kwacen wayoyi tafi ta azzara a yankunan Rijiyar Lemo, Dorayi, Sheka, Kofar mata Gwammaja da sauransu. Ko a ranar Alhamis da ta gabata al’ummar unguwannin Ƙofar Mata, Zage, Yakasai, Fagge da wasu unguwanni a cikin ƙwaryar birinin na Kano an wayi gari da irin wannan ta’asa, inda maharan suka afkawa unguwar Ƙofar Mata har zuwa ranar Juma”a ana wannan ɗauki badaɗin.
Suma al’ummar Sheka da ke makwabtaka da ƙwaryar birnin na Kano na fama da wannan babbar matsala, amma dai an samu wata gagarumar nasarar da ta kai ga damƙe babban gogarman waɗannan masu ta’annaci da ake kira Mu’azu Ɓarga, wannan matashi ya jima yana addabar wannan yankin dama unguwannin irin Medile, Shagari Kwatas, Sabuwar Gandu da sauransu.
Nasarar damƙe Ɓarga ta bayar damar samun bayannan abokansa da suke aikata wannan ɓarna, rundunar ‘yan sandan Kano sashin ‘Anty Daba’ ne suka dirarwa wannan shahararren gagararren ƙofar rago kuma aka damƙe shi, wanda yanzu haka yana hannun rundunar ‘yan sandan Kano yana taimakawa rundunar wajen damke waɗanda ya sanar da rundunar yadda suke aikata wannan ta’addanci tare.
Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar da ta gabata Al’ummar Sheka ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Muryar Jama’ar Sheka ta ziyarci Shelkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai domin jinjina wa ƙoƙarinsu.
Cikin shahararrun mafaɗatan da suka gamu da ajalinsu alokacin arangama daban-daban akwai matashin da ya addabi al’ummar Unguwar Ɗorayi mai Suna Barakita, sai kuma wani mai suna Khalufa ɗan unguwar Ƙofar Mazugal Da kuma wani guda da ke tafka irin wannan ta’asa a unguwar Gwammaja duk a kwaryar birnin Kano.
Yanzu haka dai a iya cewa faɗan daba da ƙwacen wayoyin gannu na neman zama ruwan dare a Jihar Kano, sai dai kuma rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ƙarƙashin Kwamiahinan da ke jagorantar operation ba sani ba sabo, ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan na Kano Abdullahi Haruna Kiyawa na ci gaba da samun nasarar kakkaɓe mafaɗatan tare da shiga lungu da saƙo domin farautar maɓarna
tan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp