Abubakar Abba" />

FAAC Ta Turawa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 270 A Watan Janairu –NBS

Hukumar Qididdiga ta Qasa NBS ta sanar da cewar, Kwatitin Asusun Tarayya FAAC, ya turwa Gwamnatin Tarayya jimlar naira biliyan 270.17 a cikin watan Janairun shekarar 2019.
Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin bayanan da kwamitin na FAAC ya wallafa a kafar sa ta Yanar Gizo, inda kuma bayanan suka nuna cewar, jihohin qasar nan, an tura masu jimlar naira biliyan 178.04 sai kuma qananan hukumomi sun karvi jimlar naira biliyan 133.83.
An rabarwar da matakan gwamnati uku naira biliyan 649.19 a cikin watan Janairun shekarar 2019 da aka samo daga kuxin shiga da aka samu a cikin watan Disambar shekarar 2018.
Acewar rahoton, kuxaxen sun haxa da, naira biliyan 547.46 da aka samo daga babban Asusu (SA), sai naira biliyan 100.76 daga harajin VAT sai kuma naira miliyan 976.53 daga kuxin musaya da akaci riba.
Har ila yau, an rabar da naira biliyan 45.36 ga jihohin da suke da albarkatun mai a matsayin kashi 13 bisa xari na tallafi daga gwamnatin tarayya.
Hukumomin gwamnatin tarayya da suke tarawa gwamnatin kuxaxen shiga kamar Hukumar hana fasaqauri ta qasa, Hukumar dake tarawa gwamnatin tarayya haraji ta qasa FIRS da kuma Hukumar dake sanya ido akan rabar da albarkatun man fetur DPR, ance sun karvi jimlar naira biliyan 4.69 da naira biliyan 4.04 da kuma naira biliyan 8.04 sakamakon karvo harajin da suka yi.
Dogon fashin baqin da akayi na kuxaxen da aka turwa gwamnatin tarayya ya nuna cewar, ta karvi naira biliyan 216.57 qari da kuma naira biliyan 4.81 na tallafi da kuma naira biliyan 2.43 na xauki.
Bugu da qari, naira biliyan 8.15 an turwa sashen ciyar da fannin ma’adanai sai kuma naira biliyan 5.82 zuwa ga Babban Birnin Tarayyar Abuja.

Exit mobile version