ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
3 weeks ago
Shugaban Kasa

Ofishin babban mai ba Shugaban kasa shawara ta musamman kan irin abin bajintar da dalibai suka yi,na taimakawa da ba daliban gudunmawa a fadin tarayyar Nijeriya a wani babban taro na bikin da aka yi na ranar Dalibai na kasa da kasa na shekarar 2025.

Taron mai taken, “Biki da sakama wadanda suka samu nasarakan wadansu lamurran karatun daya shafi ilimi”, dalibai an kira sune daga Jami’oi,makarantun fasaha, Kwalejojin horon Malamai, Makarantun Sakandare, da kuma Makarantar koyon aikin Lauya ta kasa.

  • Dogaro Da Noman Gargajiya Kadai Ba Zai Iya Wadatar Da  Nijeriya Ba – Farfesa Rabi’u
  • Ranchers Bees Za Su Ci Gaba Da Bugin Wasannin Gida A Filin Bako Kontagora

Da yake jawabi lokacin taron a Abuja ranar Laraba ta makon daya gabata, babban mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa kan lamarin daya shafi dalibai, Honorabul Komrade Sunday Asefon, ya bayyana muhimmanci da irin gudunmawa da ilimi yake badawa wajen gina kasa.

ADVERTISEMENT

Ya ce “Ko wadanne al’umma ana gina su ne akan kwazo, mai da hankali, da kuma hasashe na matasan da take da su. Yau, muna cikin murnar karrama wadanda suka nuna mataukar bajintar wadanda suka kammala karatu daga Jami’oinmu, Makarantun fasaha, Kwalejojin ilimi, da kuma Makarantar koyon aikin Lauya.

“Wadanda suka nuna irin wannan bajintar za su samu tallafin karatu, Komfutoci na tafi da gidanka, kudade, da kuma sauran taimako domin taimakawa irin kokarin da suke yi domin gobensu da ta wasu tayi kyau.”

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

Ya ce shi tsarin bai manta da ‘yan makarantun Sakandare ba domin kuwa suma ba’an, manta da su bane, duk wadanda suka yi wani abin bajinta an basu Naira 100,000 a matsayin wata kyauta ce domin a zaburar da su da su tuna ko ina suke akwai bukatar su ci gaba da yadda suka fara yin farar saka.

“An yi sa’ar gaske ne da kaya suka tsinke a gindin Kaba domin kuwa wannan irin abinda ko tsarin da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda tun farko ya nuna bukatar hakan ta hanyoyi dadama, wato taimako ga bangaren ilimi da kuma samun nasarar daliban Nijeriya.

“Manufar Shugaban ce daya ga tana da amfani mu kuma yau muka fito da ita fili muraran kowa ya gane da kuma ji, da take nuna dalibanmu ba kawai Shugabannin watarana bane, amma su, masu bada gudunmawa ne domin ci gaban Nijeriya ayau. Idan mun sakawa ko tallafawa wadanda suka yi fice kan lamarin da ya kai su makaranta wato karatu, tamkar muna zuba jari ne a bangaren ilimi saboda Nijeriya ta samu ci gaban da yafi na yanzu.

“Ga wadanda aka karrama yau: yadda ku ka sha gaban kowa ne wajen lamarin karatu shi yasa hakan wato abinda ya nuna da akwai fifiko tsakaninku da sauran dalibai wannan kuma yin Allah ne da kuma yardar sa. Kun nuna ko shakka babu makarantun da kuka yi sum aba kashin yadawa bane idan hara ana maganar ilimi, shi yasa ma muke la’akari da ku dangane da irin nasarorin da kuka samu. Ina kira da ku cewa kiu ci gaba kamar yadda kuka fara wajen nuna gaskiya da rikon amana, shigo da wani abinda zai amfani al’umma ta hanyar tunani mai zurfi, ku kuma tuna kuma akwai irin gudunmawar da za ku rika ba al’ummarku da kuma kasa baki daya kamar dai yadda ya jaddada,”.

Shi ma da yake ha shi bayanin Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya nuna cewa shi bikin karramawar yana nuna an san kuma ba mantawa aka yi ba da irin fadi- tashin da su wadanda suka kammala manyan Makarantun suka yi wajen neman ilimi, kamar dai yadda suke shafe dare duk saboda su yi karatun da zai taimaka masu cimma buri, sai kuma niyyar da suka daukar ma kansu da cewar cikin ikon Allah sai sun kai ga cimma burinsu kamar dai yadda ta kasance, yadda muka ga su wadannan matasan a gabanmu yau a kuma wannan lokacin.

Shi dai Minisatan ilimin mai ba shi shawara ne na musamman kan harkokin da suka shafi fasaha Dakta Dabid Atuwo, shi ne ya wkilce shi, inda kuma ya yi wata tunatarwa kan irin gudunmawa da fasaha da bada tallafin karatu suke badawa ba wajen kara taimakawa matasan domin su tashi da kasancewa masu kaifin tunani kan duk abubuwan da suka sa gabansu.

“Dangane kuma da mutum 61, da suka kammala karatunsu na Jami’oi yana yi masu kallon cewa nan gaba kadan sune za su kasance masu jan akalar yadda za’a tafiyar da abubuwa amma fa sai sai sun kara maida hankali kan karau fiye da yadda suka yi, a shekarun baya, ga shi hkan ta kai ga sun samu kasancewa da mallakar komfutar tafi- da gidanka yau,har ma ina yi maku kallon na gaba ku ne zaku ja sahun ilimin fasahar zamani cikin ikon Allah.

Ya ci gaba da bayanin cewa “ Daga cikin mutum 29 da suka samu samu tallafin karatu su yi karatun digiri na biyu kan lamarin daya shafi kimiyya, muna tare da farfesoshi, masu yi bincike, masu tsara yadda za’a tafiyar da tsare- tsaren manufofin ci gaban kasa gaba daya.”

Karamar Ministar Kudi, Ma’aikata Kudiinistry of Finance, Dakta Doris Usoka-Anite, ita ma ta yi jawabi ne kan irin gudunmawar da ake sa ran al’umma za su bada domin taimakawa wajen jin dadin dalibai lokacin suna zama a makaranta’.

Da bada tabbaci ga wadanda suka samu halartar taron cewa gwamnati zata ci gaba da tabbatar cewar duk irin tallafin da take badawa ko kuma suka kamata a bada ta bangaren ilimi, Malamai’ albashi, tsarin ciyawa a makaranta, samar da tsaro a wuraren karatu ta hanyar tsare- tsaren samar da tsaro a makarantu.

Ta ci gaba da karin bayani na cewa “Tsarin kulawa da matasan Nijeriya aiki ne da kowa ya kamata ya yi, ba kwai abin a bar wa kungiyoyin dalibai ba ko kuma ma’aikatar ilimi ba. Irin hazakar da ‘ya’yanmu dalibai suke yi, maida hankali, da kirkirar wasu abubuwa da dalibanmu su ke yi, wani abu ne da ya zama wata ‘yar manuniya ce da ke nuna lalle a samu damar sa ido ga lamarin daya shafi basirorin da suke samuwa ta hanyar ilimi.

“A yau ba muna bikin irin mizani ko darajar sarifiket na difgirin da aka yi. Muna yin biki ne yau saboda yadda Nijeriya za ta kasance a gaba cikin lamari maikyau. Maganar matasa 61 da suka kammala Jami’oi aka kuma basu kyautar Komfuta mai tafi – da gidanka, muna kallon masu ilimin fasahar hanyoyin sadarwa na zamani a matsayin sune wadanda a nan gaba za su kasance Shugabannin abubuwan da suka shafi lamarin.

“Sai kuma mutane 29 wadanda suka samu dama t an tallafa masu su yi karatun digiri na biyu a fannin kimiyya MSc ( Master of Science) ta ce , mu muna yi masu kallon Farfesoshinmu ne masu zuwa nan gaba, masu yin bincike, da kuma masu tsare- tsaren yadda manufofin ci gaban Nijeriya za su kasance. Su ‘yan makarantun Sakandare kamar yadda aka karrama su da kyaututtukan kudade, su muna yi masu kallon ko shakka babu akwai wata baiwa ta daban da Allah ya yi masu nan gaba kuma za’a kara fahimtar hakan.

“Yadda bikin nuna murnarmu ga irin nasarorin da suka samu wannan wani abu ne da yake nuna gwamnati ta kara maida hankalinta kwarai da gaske wajen tallafama wadanda idan aka basu kulawa wajen tallafin daya dace su ne a gaba za su kasance masu amfani da basirarsu wajen ci gaban kasa. Zuba jari a harkar ilimi babbar hanyar zuba jari ne wanda za’a iya yi a gaba kuma ya haifar da da mai ido a Nijeriya. Ga dukkan wadanda aka yi wa karramawar, ina masu fatan irin wannan ya zama mafarin ci gaba gare su, ba wai abin ya tsaya anan ba kamar yadda ta ce,”.

Dakta Usoka-Anite ta yi kira da daliba su maida hankalinsu kan karatu , duk kuwa da yake a yanzu akwai kafafen sadarwa na zamani da za su iya daukar masu hankali.

Ta yi kira da dalibai gaba daya cewar “ Su yi amfani da duk wata basirar da Allah ya basu kwarai da gaske kamar yadda ya dace. Ko kana da kokari ko wata hazaka a bangaren karatum ko wasanni,, waka, ko fasaha ta yin ayyukan gida, ka yi kokarin yin abinda zai kira maka girma, ka nunawa duniya cewar ka iya abin sosai,”.

Tallafin karatu na masu yin digiri na biyu damar an ba wadanda suka fi kowa kokari a jarabawar kammala Jami’a an kuma yi amfani ne da sassan shida da ake da su, a Nijeriya, da suka hada da Jami;ar gwamnatin tarayya Dutsin-Ma a Arewa maso yamma, Jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Lokoja Arewa ta tsakiya, Jami’ar Olabisi Onabanjo a Kudu maso yamma, Jamii’ar Jihar Ribas, Kudu maso Kudu, Jam’ar Fasaha ta gwamnatin tarayya Ower a Kudu maso gabas, da kuma Jami’ar gwamnatin tarayya a Wukari sashen Arewa maso gabas.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Majalisar Wakilai Ta Nemi A Ɗauki Sabbin Ma’aikata A Jami’o’in Nijeriya
Ilimi

Majalisar Wakilai Ta Nemi A Ɗauki Sabbin Ma’aikata A Jami’o’in Nijeriya

November 21, 2025
Next Post
Yadda Gwamnatin Tarayya Da Wasu Jihohi Suka Rufe Makarantunsu Kan Matsalar Tsaro

Yadda Gwamnatin Tarayya Da Wasu Jihohi Suka Rufe Makarantunsu Kan Matsalar Tsaro

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Shugaban Somaliya: Kara Fadada Bude Kofa Ga Kasashen Waje Da Sin Ke Yi Zai Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

Shugaban Somaliya: Kara Fadada Bude Kofa Ga Kasashen Waje Da Sin Ke Yi Zai Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.