Fahimta Fuska

tare da Sheikh Ibrahim Khalil

A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko nasirsgwangwazo@yahoo.com ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08036365416.

Assalamu alaikum.  Don Allah Malam, idan al’amura suka tabarbarewa mutum ta fuskar kasuwancinsa ko kuma wasu harkoki nasa, me ya kamata ya yi?

Abin da ya kamata ya yi da farko shi ne, ya samu kwararrun mutane masu hankali da suka fahimci al’amuran rayuwa ya fada musu gaskiyar abin da ke faruwa a kan harkar kasuwancinsa da yake yi su ba shi shawara a kan harkokin nasa, sannan ya duba yanayin yadda yake kashe kudadensa, akwai kuskure ko babu, yana da tattali ko babu. Dalili kuwa a nan abubuwa guda uku ne, dole ne ka koyi yadda ake kashe kudi, yadda ake yin tattali da tanadi da kuma yadda ake yin neman kudin, ma’ana kasuwanci. Saboda haka, dole ne a koma a duba yadda ake yin wadannan abubuwa guda ukun a gani cewa daidai kake yin su ko kuwa sabanin haka kake yi. Sannan abu na gaba shi ne, ka dage da yin zikirin Allah da istigfari ko salatin Annabi ko Ya hayyu Ya kayyum bi rahmatika astagisu da dai sauran zikirai da salatan Annabi (SAW).

 

Assalam Malam, wani lokaci idan sha’awa ta kamani, wani farin ruwa yakan fito daga zakarina amma ba maniyyi ba ne. Malam, a nan wanka zan yi ko kuwa tsarki zan yi?

A nan dubawa za a yi, idan ruwan nan da ya fito daga gabanka fari ne kamar madara, a nan wanka za ka yi, idan kuma fari ne ba kamar madara yake ba ma’ana kamar ruwa, ba za ka yi wanka ba sai kawai ka yi tsarki ka kuma wanke duk inda ya baci a jikinka.

Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wabarakatuhu. Jawabin da Malam ya yi a kan neman maganin mazakuta, don Allah Malam ya taimaka min na dade ina fama da wannan matsala sakamakon wasa da nake yi da gabana, gabana ya motes ya zama dan karami sannan ina yin saurin inzali, maniyyina ya zama ruwa-ruwa, na sha magunguna da dama amma har yanzu babu wani labara. Don Allah Malam a taimaka min ina cikin mawiyacin hali, idan da hali zan so na ga Malam don na yi masa karin bayani.

Kamar yadda na sha fada ne ba za mu zama kamar ‘yar maiganye ba, idan muka baiwa mutane dama ko shakka babu za su maida mu ‘yar maiganye. Abin da kawai za mu fada maka shi ne, ka rika shan zuma babban cokali kafin ka ci abincin safe da na rana da kuma na dare. Ka tabbata ka sha babban cokali kafin ka kai ga cin abinci, haka nan idan za ka kwanta barci a nan ma sai ka sha babban cokali ka kwanta, kazalika ka rika cin naman kaza gwargwadon iko, ma’ana koda cinya daya ce musamman da yamma, ka kuma rika shan madara (fresh milk) kofi daya da safe daya da yamma. Maganar gani na kuma, ba ma so mu bayar da wannan kofa, don haka ka fara yin amfani da wadannan abubuwan da na fada maka insha Allahu za a ga fa’idar abin, Allah Ya sa a dace, amin.

 

Assalam Malam, don Allah wadane addu’o’I mutum zai rika yi lokacin da yake yin Sallah don kawar da tunani ko wasiwasi?

Babu wata addu’a da za a ba ka, don kuwa ai babu wanda ya isa ya yi Sallah ba tare day a yi tunani ba, kawai dai ya yi kokari tunaninsa a Sallar ya zama tunani ne mai kyau. Amma babu wani mahaluki day a isa ya yi Sallah ba tare da ya yi tunani ba, dole ne sai mutum ya yi tunani. Saboda haka duk wanda y ace da kai idan za ka yi Sallah kada ka yi tunani, shi ma karya yake yi don kuwa idan shi ma zai yi Sallar sai ya yi tunani. Kokarin kadai da za ka yi shi ne, kada ka yi wani tunani wanda shari’a ba ta so, ma’ana kada yi tunani mara kyau ko wanda ya sabawa shari’a ko wani abu makamancin haka, duk tunanin da za ka yi ka tabbata tunani ne na wani abin alheri ban a sharri ba. Idan tunanin sharrin ya bijiro maka yayin Sallah, sai ka yi maza-maza ka kawar da shi sannan ka yi kokarin bijiro da na alheri don kada shaidan ya samu galaba a kan ka.

Exit mobile version