A baya bayan nan ne aka yi bikin bude cibiyar koyar da harshen Sinanci da kamfanin gine-gine na kasar Sin na CRCC ya yi wa kwaskwarima, a makarantar sakandare ta Garki Area 11 dake Abujan Nijeriya.
Haka zalika a jiya, an yi bikin bude kwalejin Confuscious a jami’ar Alkahira dake Masar, don kaddamar da shirin koyar da harshen Sinanci.
Bambancin harshe babban kalubale ne dake karan tsaye ga kusan kowacce mu’amala, sannan fahimtar juna, ita ce tushen ingantacciyar dangantaka da za ta tabbatar da dorewarta.
Muddin aka samu fahimtar juna ta fuskar al’adu da harshe, to za a samu zaman lafiya da ci gaba tsakanin bangarori daban daban. A nan gaba, cikin shekaru kalilan, al’ummomin Sin da Afrika za su dunkule.
Shirye-shiryen na koyar da harshen Sinanci a Nijeriya da Masar, sun shafi makarantu ne na sakandare, wannan kuma ya nuna kaifin basirar Sin na mayar da hankali kan yara manyan gobe.
Kamar yadda ake cewa, da zafi-zafi a kan daki karfe, wato fahimtar al’adun Sin da ma harshen Sinanci ga yara a nahiyar Afrika, za ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina al’ummar Sin da Afrika ta bai daya, kuma mai kyakkyawar makoma.
Wasu za su ce, to shin ita kasar Sin tana koyar da harsunan Afrika a kasarta? Abun burgewa shi ne, kasar ta shafe gomman shekaru tana koyar da harsunan Afrika, har dalibai na samu shaidar digiri a harshen Hausa da sauran wasu harsunan Afrika kamar Kiswahili. Baya ga haka, da idona, na ga wani littafin karatu na daliban ajin firamare, dake dauke da harshen Hausa.
A sannan nan kara fahimtar lallai Sin ta yi nisa a kokarinta na habaka dangantaka da Nijeriya da ma sauran kasashen Afrika.
Ilimi shi ne gishirin rayuwa. Haka kuma kashin bayan ci gaban kowacce al’umma. Yadda gwamnati da kamfanonin kasar Sin ke mayar da hankali wajen bayar da gudunmawa ga kyautatuwar ilimi a Nijeriya da sauran kasashen Afrika, ya cancanci yabo, domin lamari ne da za a ga alfanunsa a nan gaba.
Kamar yadda shugaban hukumar ilimi a matakin farko ta birnin Abuja, Alhassan Sule ya bayyana, daddadiyar dangantakar Sin da Nijeriya ta taimaka sosai ga aikin samar da ilimi a kasar. (Fa’iza Mustapha)