Babu wani abu da ya gwada irin tsayin daka kan manufofin harkokin wajen Nijeriya a tsawon shekara 67 da kuma kwarewa, hangen nesa da kuma fahimtar manufofin Nijeriya daga ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar, kamar sauyin gwamnati da aka yi a jamhuriyar Nijar ba bisa ka’ida ba, da kafa kungiyar kawancen kasashen Sahel, AES, da kuma irin halin tsokanar da gwamnatin mulkin soja take yi wa Nijeriya.
Ba wai bisa hadari ba ne ya sa Nijeriya ta iya daukar matakai wajen iya tafiyar da rikicin diflomasiyya da gwamnatin mulkin sojan Nijar, Burkina Faso da kuma Mali. Tambayar da ya kamata a yi a nan ita ce: mene ne sirrin, kuma mene ne lakanin, da har Nijeriya ta yi na magance matakan bata suna, barazana da kuma farfaganda na AES?
- Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
Ana iya samun wannan amsar a cikin rubutun da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yi mai taken “Manufar Harkokin Waje da Hanyar Zaman Lafiya Da Makwabciya Mai Hatsari”. Wannan rubutun zai bube ido ga duk mai sha’awar fahimtar manufofin Nijeriya a kasashen waje.
Daya daga cikin manufofin shi ne – “Habaka dokokin kasa da kasa da wajibcin yarjejeniya”. A sakamakon haka matakin da Nijeriya ta dauka wajen kakaba wa gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar takunkumi ya kasance a karkashin wannan manufa.
Ministan ya yi taka-tsan-tsan wajen tunatar da mu cewa: “Tsarin mulki (kuma) ya bayyana dalilin da ya sa duk wata gwamnatin Nijeriya da ke da iko za ta damu matuka idan makwabciyarta ta kasance tana gudanar da mulki ba tare da kundin tsarin mulki ko ka’ida ba”. Abin da hakan ke nufi shi ne, a tsarin mulki, ya zama wajibi Nijeriya a matsayinta na memba a kungiyar ECOWAS ta mutunta tare da inganta yarjejeniyoyin ECOWAS da ka’idoji da sauran dokokin kasa da kasa.
Babban sakon ministar shi ne cewa manufofin harkokin waje na Nijeriya sun ginu ne a kan tsarin mulki da bin doka da oda. A yayin da Nijeriya ke mutunta ka’idojin zirga-zirgar al’umma na ECOWAS, Jamhuriyyar Nijar, a shekarar 2015, alal misali, ta je ta ayyana wata doka kan ‘yan ci-rani da ta saba wa ka’ida. Shin wannan bai isa ba ya nuna wane ne yake mutunta doka ba?, da kuma wane ne wanda ba ya mutunta doka?
Dangane da yadda ake amfani da diflomasiyya da sauran hanyoyin da dimokuradiyya ta tanada, ministan ya bayyana a cikin rubutunsa, irin abubuwan da gwamnati ta yi na magance batutuwan da suka shafi mulkin sojan Nijar da sauran membobin kungiyar AES.
Amma duk da haka wasu masu suka na ci gaba da tabbatar da taurin kai da rashin hadin kai daga gwamnatin mulkin soja kan takunkumin da aka kakaba wa masu satar mulki. A lokaci guda kuma, wadannan masu suka da tada jijiyar wuya sun ki amincewa da irin matakan lallami da hankali da aka nuna wa masu mulkin sojan.
Wani muhimmin batu na rubutun ministan shi ne “Tsarin cin gashin kai” a matsayin ginshiki na manufofin gwamnatin Tinubu. Nijeriya na da hakki da ‘yanci, kuma tana da hakkin yin hulda da kowacce kasa ba tare da wani ya fada mata, ko ya jagorance ta ko umurtar ta ba. Dole ne Nijeriya ta yi aiki tare da gabas da yamma, da dukkan manyan kasashe. Nijeriya ba ta nuna wariya a manufofinta na kasashen waje. Jamhuriyar Nijar, ko wata kasa ba za ta zayyana mana kasashen da za mu yi hulda da su ba.
Habaka hadin kan Afirka da goyon bayan hadin kan Afirka ya kasance wani abu muhimmi kuma na dindindin a manufofin harkokin waje na Nijeriya kamar yadda ministan ya bayyana. Nijeriya memba ce ta ECOWAS da AU – kuma dukkanninsu suna aiki ba dare ba rana domin ganin an samu hadin kai, ta hanyar amfani da tsarin bi a hankali kuma mataki-mataki.
Abu mafi muhimmanci, ministan ya kuma tunatar da wadanda suke yada zarge-zarge marasa tushe balle makama a kan Nijeriya da cewa “A halin yanzu Nijeriya na da sojoji a ayyukan wanzar da zaman lafiya a Guinea Bissau da Gambia. Nijeriya kuma ita ce ke kan gaba wajen tabbatar da rundunar ECOWAS a matsayin masu jiran ko ta kwana, duka wannan a kokarinta na yaki da ta’addanci da rashin zaman lafiya a yankinmu a karkashin doka”.
- Kwamared Bishir Dauda, Sabuwar Unguwa Katsina.