• English
  • Business News
Saturday, September 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [2]

by Nuhu Ubale Ibrahim
7 months ago
in Addini, Ilimi
0
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manufar Saukar da Alƙur’ani:

“فَاعْلَمْ أَنَّ الْمَقْصُودَ بِالْقُرْآنِ دَعْوَةُ الْخَلْقِ إِلَى عِبَادَةِ اللَّهِ وَإِلَى الدُّخُولِ فِي دِينِهِ.”

Fassara:

“Ka sani, manufar saukar da Alƙur’ani ita ce kira ga halittu su bauta wa Allah kuma su shiga cikin addininsa.” Duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzili [1/5]

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1]
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]

Sharhi:

Labarai Masu Nasaba

Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO

Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

Shehun malami al-Imam Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Alƙur’ani ya sauka shi ne kira ga bautar Allah da shiga cikin addininsa. Wannan magana tana da tushen ilimi mai zurfi wanda ke da nasaba da tauhidi da shari’a, da hikimar shiriya.

1. Tauhidi a Matsayin Asalin Kiran Alƙur’ani: Manufar farko da Alƙur’ani ya zo da ita; ita ce tabbatar da tauhidi, wato bautar Allah Shi kaɗai ba tare da sanya masa abokin tarayyaba. Wannan ita ce mafi girman sako da dukan annabawa suka zo da shi. Allah ya ce: “Kuma babu wani Manzo da Muka aiko a gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa: Lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Ni, to sai ku bauta mini.” Suratul Anbiya aya ta 25. Saboda haka, Alƙur’ani ya sauka ne domin ya tabbatar da cewa halitta ta san cewa akwai Mahalicci guda ɗaya, kuma Shi kaɗai ya cancanci bauta. Wannan kira yana nufin a fitar da mutane daga duhun shirka da jahilci zuwa ga hasken tauhidi da sanin Allah.

2. Shiga Cikin Addinin Allah: Manufar Alƙur’ani ta bautar Allah za ta samu ba sai a cikin addinsa. Don haka sai an shiga cikin addininsa da shari’ar da ya saukar, wato addinin Musulunci. Wannan yana nufin a bi dukan dokokin Allah da shari’o’in da suka zo a cikin Alƙur’ani da Sunnah. Allah Yana cewa: “Lalle addini a wurin Allah shi ne Musulunci.” Suratu Ãli Imrãn aya ta 19. Kuma ko mutum ya yarda da bautar Allah amma bai karɓi Musulunci ba, to Allah ba Zai karɓa masa ba, domin Ya ce:” Duk kuma wanda ya nemi bin wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karɓa daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru ” Suratu Ãli Imrãna aya ta 85. Wannan yana nuna cewa manufar Alƙur’ani ita ce shiryar da mutane su shiga cikin Musulunci ta hanyar yin imani da Allah da biyayya ga umarninsa.

3. Alƙur’ani A Matsayin Hujja: Saukar da Alƙur’ani yana ɗauke da cikakken tsarin rayuwa wanda yake jagorantar Musulumi a cikin dukan al’amuransu. Ya ƙunshi dokokin ibada kamar sallah da azumi da zakka da kuma hajji, da sauran su. Kuma ya ƙunshi dokokin mu’amala kamar ciniki da aure da kasuwanci, da sauran su. Hakanan Ya ƙunshi kyawawan ɗabi’u kamar gaskiya da zumunta, da , haƙuri da adalci da roƙon amana da sauran su. Kuma ya ƙunshi hukunce-hukunce da shari’a kamar halas da haram. Wannan yana nuna cewa saukar da Alƙur’ani ba wai kawai don sanin Allah ba ne, har ma don rayuwar duniya da lahira.

4. Manufar Saukar da Alƙur’ani ta Ķunshi dukan Halitta: Saukar da Alƙur’ani haske ne ga duniya baki ɗaya, mutane da aljanu, da ƙwari da dabbobi da halittu baki ɗaya, domin dukansu su san hanyar shiriya. Saboda haka, yana kira ga: da bin Alƙur’ani, kowa ya yi imani da Allah kaɗai ne abin bauta ba tare da an sanya masa kini ba. Mushrika da Ahlul Kitabi, wato Yahudu da Nasara da Maguzawa da kowa da kowa da su kaɗaita Allah da bauta, su shiga addininsa, kuma su bi shiriyarsa a kowane al’amari na rayuwarsu.

A taƙaice, wannan magana ta Ibnu Juzai tana bayani a kan cewa Alƙur’ani ya zo ne domin:

1. Kiran mutane su bauta wa Allah shi kaɗai,

2. Shiriyar da mutane zuwa ga addinin Musulunci,

3. Tabbatar da doka da tsarin rayuwa mai cike da adalci,

4. Fitar da mutane daga duhun jahilci zuwa hasken shiriya, domin samun jin daɗin duniya da lahira.

Wannan shi ne babban abin da Alƙur’ani ya zo da shi, kuma dukkan surori da ayoyinsa suna bayani ne akan waɗannan ginshiƙai.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abu Razina Nuhu Ubale PakiAl-Qur’anAlƙur’aniIbnu JuzaiRamadanTafsirin Alƙur’aniTafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Yi Cikakken Zama Na Uku Na Taron Shekara-Shekara Na Majalisar Bada Shawarwari Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin

Next Post

Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria

Related

Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO
Ilimi

Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO

1 week ago
Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe
Ilimi

Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

2 weeks ago
Kwamitin JAMB Ya Bankaɗo Magudin Jarabawa A 2025 UTME
Ilimi

Kwamitin JAMB Ya Bankaɗo Magudin Jarabawa A 2025 UTME

3 weeks ago
ASUU
Ilimi

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU

3 weeks ago
Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

3 weeks ago
Lambar Yabo Ta CON: Buni Ya Zama Zinare Bashi Da Maboya
Ilimi

NTIC Ta Jinjina Wa Gwamna Buni Kan Taimako A Bangaren Ilimi

4 weeks ago
Next Post
Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria

Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

September 27, 2025
Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance

NDLEA Ta Farmaki Masu Safarar Muggan Kwayoyi A Sassan Nijeriya

September 27, 2025
Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

September 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Mutum Hudu Kan Satar Taransifoma A Makaranatar Kebbi

‘Yansanda Sun Cafke Mutum Hudu Kan Satar Taransifoma A Makaranatar Kebbi

September 27, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Sabon Farashin Jigilar Mahajjata A 2026, Ƴan Arewa N8.2m, Ƴan Kudu N8.5m

Sabon Farashin Jigilar Mahajjata A 2026, Ƴan Arewa N8.2m, Ƴan Kudu N8.5m

September 27, 2025
Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma

Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma

September 27, 2025
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan

Lalacewar Tsarin Zabe Babbar Barazana Ce Ga Dorewar Dimokuradiyyar Afirka — Jonathan

September 27, 2025
Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka

Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka

September 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.