• English
  • Business News
Wednesday, July 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]

by Nuhu Ubale Ibrahim
4 months ago
in Addini, Ilimi
0
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abubuwan da Suke Hana Mutum bin Allah:

“القَواطِعُ عَنِ اللهِ أَربَعَةٌ: الشَّيطانُ، وَالنَّفسُ، وَالدُّنيا، وَالخَلقُ. فَعِلاجُ الشَّيطانِ: الاِستِعاذَةُ وَالمُخالَفَةُ لَهُ، وَعِلاجُ النَّفسِ: بِالقَهرِ، وَعِلاجُ الدُّنيا: بِالزُّهدِ، وَعِلاجُ الخَلقِ: بِالاِنقِيادِ وَالعُزلَةِ.”

Fassara:

“Abubuwa huɗu ne ke katange mutum daga bin Allah: Shaidan da son zuciya da duniya, da halittu (wato mutane). Maganin Shaiɗan shi ne: saɓa masa da kuma neman tsarin Allah a kansa, maganin son zuciya kuma shi ne: fin ƙarfin ta da taƙwara ta ta bi gaskiya. Maganin duniya kuma : shi ne guje wa ƙyaleƙyalenta da ruɗinta. Maganin mutane kuma: karkata ga Allah Shi kaɗai da nisanta kai yin biyayya da nisanta kai daga mutane (ɓatagari)” Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/30].

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [2]
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]

Fashin Baƙi:

Labarai Masu Nasaba

Abinda Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (9)

AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

Wannan magana ta al-imam Ibnu Juzai tana bayani ne kan abubuwa huɗu da ke hana mutum bin Allah da kuma yadda za a magance kowanne daga cikinsu. Ga ƙarin haske akan haka:

1. Shaiɗan: Shaiɗan shi ne abokin gaban mutum na ƙoli tun daga haihuwarsa har mutuwarsa. A matsayinsa na maƙiyi, burinsa shi ne ya ɓatar da mutum daga bin Allah. Yana amfani da hanyoyi daban-daban kamar waswasi, da sanya shubuha, da ƙarya, da kawar da zuciya daga ibada, da sanya shakku a cikin imani, da sauran makirce-makircensa. Allah Ya umurce mu da kada mu bibiyi tafarkin shaiɗan a rayuwarmu.

Maganin Shaiɗan: Babban maganin Shaiɗan shi ne neman tsari da kariya a kansa a wurin Allah, da sɓa masa, Wato mutum ya yi ƙoƙarin yin akasin abin da Shaiɗan ke umarta. Idan Shaiɗan yana kiran mutum zuwa ga zunubi, ya yi ƙoƙarin kaucewa.

2. Son Zuciya: Zuciyar mutum tana da buƙatu da sha’awa, kuma tana iya karkatar da shi daga tafarkin gaskiya. Idan mutum bai kula ba, zuciyarsa za ta janyo masa son abin da bai dace ba, ko kuma nuna ƙyama ga abin da Allah ya shar’anta wanda hakan zai kai mutum da barin Allah da addinsa. Don haka; dole ne mutum ya kula da gyaran zuciyarsa.

Maganin Son Zuciya: Maganin son zuciya shi ne mutum ya fi ƙarfin ta, Wato mutum ya tilasta wa zuciyarsa bin gaskiya, ko da kuwa tana son akasin haka. Tanƙwara ta ta bi gaskiya, yana nufin horar da zuciya kan gaskiya da bin umurnin Allah. Hakan na faruwa ne ta hanyar tilasta wa kai yin biyayya, ta hanyar salla da azumi, da ambaton Allah, da kasancewa cikin kyawawan ayyuka tare da addu’a Allah Ya tsarkake ta.

3. Duniya: Duniya tana da ruɗi da ƙawanyar ƙyaleƙyale, tana janyo hankalin mutum zuwa ga jin daɗi kamar samun dukiya, ko matsayi, da sauran abubuwan da ke iya karkatar da shi daga bin Allah. Allah ya bayyana cewa duniya ruɗi a wurare daban-daban a cikin Alƙur’ani, hakanan Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan ruɗin da duniya take yi wa mutane.

Maganin Duniya: Guje wa ƙyaleƙyalenta da ruɗinta, Wato mutum ya fahimci cewa duniya ba ta da daraja idan aka kwatanta da lahira, kuma bai kamata ya jefa kansa cikin ruɗinta ba, domin ba ta da tabbas. Mutum ya kasance mai tsoron Allah da ƙoƙarin bin dokokinsa a kowane hali.

4. Halittu (Mutane): Mutane na iya zama sanadin da zai hana mutum bin Allah, musamman idan yana koyi da su a kan abin da ba daidai ba. Akwai waɗanda za su janyo mutum cikin halayen banza ko su hana shi aikata alheri, ta yadda hakan zai lalata masa zuciya, domin zama da maɗaukin kanwa yana kawo farin kai.

Maganin Mutane: Karkata ga Allah Shi kaɗai, wato mutum ya yi ƙoƙarin maida hankalinsa ga Allah kaɗai, ba wai ya dogara da mutane ko kuma ya dinga yin abubuwa don faranta musu ba. Hakanan mutum ya nilisanci biyayya ga mutane idan a cikin abin da yake ɓata; Idan mutane suna jagorantar mutum zuwa ga ɓarna, ya kamata ya guje musu.

Zaɓar abokai nagari yana taimaka wa mutum wajen zama nagari. Ya zaɓi waɗanda za su taimaka masa wajen bin Allah, ba waɗanda za su janye shi zuwa ga halaka ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abu Razina Nuhu Ubale PakiAl-Qur’anAlƙur’aniIbnu JuzaiTafsirin Alƙur’aniTafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Sakataren Baitul Malin Amurka

Next Post

NNPC Da Dangote Na Shirin Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Kan Sayen Ɗanyen Mai

Related

Abinda Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (9)
Ilimi

Abinda Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (9)

4 days ago
AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate
Ilimi

AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate

1 week ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)
Ilimi

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)

2 weeks ago
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)
Addini

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

2 weeks ago
JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don Ɗaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa
Ilimi

JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don Ɗaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa

3 weeks ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (7)
Ilimi

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (7)

3 weeks ago
Next Post
NNPC Ya Samu Ribar Naira Tiriliyan 3 A 2023

NNPC Da Dangote Na Shirin Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Kan Sayen Ɗanyen Mai

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

Omokri Da Sarki Sun Soki Obi Saboda Rashin Halartar Jana’izar Buhari

July 16, 2025
Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3

Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3

July 16, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

July 16, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno

July 16, 2025
Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?

EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari

July 16, 2025
Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

July 15, 2025
Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

July 15, 2025
VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

July 15, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

July 15, 2025
An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

July 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.