Kamar yadda muka yi bayani a baya, Azumin watan Ramadana wajibi ne ga dukkan Musulmi baligi mai lafiya ba mara lafiya ba, wajibcin azumi kamar yadda Allah ya fada acikin Al’kur’ani da fadarsa yana cewa: “Ya ku Muminai Allah Ya wajabta muku yin azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin ku, ko za ku ji tsoron Ubangijinku.
Kwanaki ne kididdigaggu, wanda ya kasance a cikinku bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya rama abin da ya kubuce masa a wasu ranakun, wadanda kuma ba za su iya yin azumin ba, to su ciyar da Miskinai, amma wanda yake da damar ciyar da miskinai da yawa, to ya yi alkairi ne a wajenshi, lallai yin azumin ya fi alkairi a gare ku, idan kun san wannan alkairin da ke cikin azumin.
“Lallai watan Ramadana da aka saukar da Alkur’ani a cikinshi, shiriya ne ga mutane, sannan kuma akwai ayoyi bayyanannu a cikinshi masu shiryarwa zuwa ga Allah da bayyana hukunce-hukunce. Duk wanda ya halarci ganin watan to ya azumce shi, wanda kuma bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya biya abin da ya tsere masa a cikin sauran wasu ranakun, Allah sauki yake nema daga wurinku ba wahalarwa ba, Allah yana son ku cika adadin azumin, sannan yana son ku yi masa kirari daga abin da ya shiryar da ku, ko za ku gode masa?”.
Yana daga cikin falalar azumi, cewa yana sa tsoron Allah sabida yana karya sha’awa, yana daga cikin fa’idar azumi, Allah ya ce don mu yi takawa: Takawa, mataki-mataki ce, akwai ta gama-gari da ta kebantattu da ta kebantattun kebantattu.
Takawa ta gama-gari: ita ce ta a bar ci da sha har izuwa faduwar rana, sannan da yin aiki don neman lada da bari don neman leda. Wannan takawar ba ta hana wasu yin abin da bai dace ba.
Takawa ta kebantattu: ita ce a bar ci da sha har izuwa faduwar Rana, yin ayyuka don Allah, sannan ba za su yi karya ba, ba za su yi husuma ba, ba za su yi cece-ku-ce ba. Za su shiga cikin ibada ta ko’ina.
Takawa ta kebantattun kebantattu: sun hada duk abin alkairi na gama-garin mutane, sun hada duk abin alkairi na kebantattu sannan sun kara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah, ba su ganin wanin Allah, a ko da yaushe suna Fadar Allah ko suna Fadar Annabi (SAW) ko suna fadar Waliyyan Allah.
Wadannan Takawa guda Uku, Allah ya fada mana su cikin Alkur’ani yana cewa : “Ba laifi ga wadanda suka yi imani da Allah suka yi aiki mai kyau cikin abin da suka ci, idan suka yi takawa suka yi Imani, sannan suka yi wata takawa kuma suka yi Imani sannan suka yi wata takawa sannan suka yi kyautaye.”
Ayar ta sauka ce lokacin da ayar haramta giya ta sauka, sai wasu daga cikin Mu’uminai shubuha ta kama su suke cewa “to yanzun ‘yan uwanmu Muminai da suka sha giya a baya fa, kuma ga shi sun mutu yanzun, to ya za a yi kenan yanzun? Sai Allah ya saukar da wannan ayar yana mai cewa ba laifi a gare su tunda sun mutu lokacin ba a haramta giyar ba.
Alhamdulillah, duk wadannan takawa guda Uku, suna daga cikin falalar Ramadana. Takawa cikin Islam, Takawa cikin Iman sai Takawa cikin Ihsan.
Azumin Ramadana, kwanaki ne kididdigaggu, wata daya ne kacal cikin watanni sha biyu, kuma Allah ya bayyana mana cewa ya san akwai marasa lafiya a cikinmu, kuma akwai matafiya a cikinmu, to sai su kididdige kwanakin da azumin ya tsere musu, su rama a wasu kwanakin.
Ayar da tagabata ta bayyana wajibcin azumin watan Ramadana a Kur’ani, sai kuma hadisi mai zuwa, zai tabbatar da wajibcin azumin watan Ramadana a Sunnah Ta Annabi (SAW).
“An gina musulunci a kan shika-shikai guda biyar: 1- Shaidawa babu wani Ubangiji da ake bautawa da gaskiya sai Allah, da Shaidawa Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne 2- Sai Tsaida Sallah, 3 – Ba da Zakka 4- Azumin watan Ramadana 5– Sai Ziyartar Dakin Allah mai girma.”
Ya zo a cikin Hadisin Dalhatu bin Abdullahi, cewa “wani Mutum ya tambayi Annabi (SAW) yana mai cewa ya Ma’aikin Allah, gaya min abin da Allah ya wajabta min na daga azumi, sai Annabi ya ce Watan Ramadana, sai Mutumin Ya kara cewa akwai wani kuma da Allah ya kara wajabta min, sai Annabi ya ce A’a sai dai in za ka yi azumin Nafila.”
Babu jayayya a duk jama’ar musulmi kan wajibcin azumin watan Ramadana.
An wajabta azumin watan Ramadana ranar Litinin, dare biyu da suka shige na watan Sha’aban bayan Hijira. Annabi SAW bayan ya yi Hijira zuwa Madina daga Makkah a cikin watan Rabi’ul Awwal, aka tafi zuwa Rabi’us sani har zuwa Zulhajji, sannan aka juyo Muharram har zuwa Ramadan, a cikin shekara ta biyu kenan da Hijira aka wajabta azumin watan Ramadan.
Alhamdulillah, abin da ya gabata shi ne bayanin azumi daga littafin Allah da Sunnar Annabi Muhammad (SAW) da hadin kan al’ummar musulmi gaba daya cikin wajibcin azumi.
Nasa’i ya ruwaito, Abi Umamata ya ce “Ya Ma’aikin Allah, horar ni da wani aiki kebantacce wanda zan kebanta da shi, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, na hore ka da yin azumi, bayan Farillah ka dinga yin na nafila, sabida shi azumi ba shi da kama cikin Ibada.” Sabida kowacce Ibada wasa zai iya shigar ta amma ban da azumi.
Wannan ya nuna alakar Ubangiji da azumi, sabida Ubangiji babu misalinsa kamar yadda azumi sh ima babu misalinsa.
Muslim ya fitar cikin Sahihinsa daga Abi Hurairata ya ce: Manzon Allah SAW Ya ce “Ubangiji Ya ce dukkan Ibada ta Dan’adam ce, sai dai azumi nawa ne, kuma ni ne zan saka masa da wannan. Don ni ya yi, to ni zan saka masa.”
Ya zo cikin Hadisi cewa “Azumi garkuwa ne (tsari ne daga Shaidan, daga wuta, daga dukkan abubuwa masu cutarwa), idan dayanku yana azumi, kar ya fadi maganar da ba ta dace ba, kar ya yi hayaniyar da ba ta dace ba, idan wani ya zage shi ko ya nemi husuma da shi, to ya ce ni mai azumi ne, na rantse da wanda ran Annabi Muhammad (SAW) ke hannunsa, warin bakin mai azumi shi ya fi kamshi ranar Lahira a wurin Ubangiji daga turaren almiski”
Muslim ya fitar cikin Sahihinsa daga Sa’adu ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce: “A cikin Aljannah akwai wata kofa ana kiranta da suna kofar koshi (Rayyanu), ba masu shigar ta sai masu azumi”
Mu sani yaku ‘yan uwa, Allah ya amsa mana azuminmu na Ramadana, Allah ya karfafe mu da wannan kissa cewa, Ma’anar azumi ‘kamewa ko daukakawa’. Azumi ibada ce da babu misalinta kamar yadda Ubangiji ba shi da misali, kowacce ibada cewa ake ‘na yi’ – na yi sallah, na yi zakkah, na yi sadakah na yi… amma azumi sai dai a ce ‘na bari’ – Na bar ci, na bar sha, na bar saduwa da iyali na bar… haka Rabbul izzati shi ma sai dai ka ji babu da, babu iyali, ba ya ci, ba ya sha ba, ba, ba da sauransu.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa cikin yardar Allah.
Alhamdu Lillah.