• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Allah Ya Fi Son Kyawawan Ayyukan Da Aka Yi A Kwanakin

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
12 months ago
in Dausayin Musulunci
0
Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Allah Ya Fi Son Kyawawan Ayyukan Da Aka Yi A Kwanakin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yana daga falalar wadannan kwana goma na farkon watan Zulhajji, su ne cikamakon watanni sanannu na aikin Hajji.

Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce Hajji watanni ne sanannu. Tun daga Shawwal watan Hajji ya shiga, yanzu in ka yi umura da azumi ba za ka yi hadaya ba, ba ta hau kanka ba, amma kana shigowa Makka sai aka sanar da ganin watan Sallah (Shawwal), idan ka yi umura to ka yi ta a cikin watan Hajji sai ka yi hadaya. Watannin Hajji su ne Shawwal, Zulkida da Zulhajji, wadannan kwanaki goman na farko su ne cikon lokacin Hajji.

  • Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (1)
  • Girman Darajar Manzon Allah SAW Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (7)

Tun da Arfa an yi ta ranar 9 ga wata, jifa da dawaful ifada an yi su ranar 10, to Hajji ta kare, sauran ayyukan da za a yi nafila ne kawai.

Sannan kwana goman nan na farkon watan Hajji su ne kwanuka sanannu da Allah ya shar’anta yin zikirai a cikinsu, saboda ni’imar kayan dadi da ya ba mu. Allah bai hore ma wani a duk tsawon shekara ya iya sayen nama ya ci a gidansa ba, amma lokacin layya Allah na iya hore masa ya sayi abin layya ko kuma wani ya yi layyar ya ba shi sadakar nama. To a bisa wannan ni’ima a yi ta zikiri tun daga farkon wata har zuwa karshen kwanukan sanannu. Zikiran da ake yi a cikin wadannan kwanukan sanannu sun fi falala a kan na wasu kwanukan da ba su ba. Kila an ce sun fi falala da kwana dari uku da sittin (kimanin shekara kenan). Kila kuma sun fi da kwana dubu. Ba zikirai ba kawai, duk wani aikin alheri ma a cikin wadannan kwanukan suna da wannan falalar. Shi ya sa Bayin Allah tun daga kan Sahabbai da Shehunnai idan wadannan kwanukan suka kama, sukan yawaita zikiran da suke yi, har wasu na shiga cikin kasuwanni suna yawo suna zikiri, masu kasuwar ma suna amsa musu, saboda kwanukan na zikiri ne. Bare kuma a ce ranar Arfa da wadannan kwanukan na yanyana nama (Ayyamut Tashrik). Galibi mu nan (a Maz’habar Malikiyya ga wadanda ba su je Hajji ba) sai ranar Sallah da Azuhur ake fara zikiran (Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamdu) zuwa Sallar Asubahin rana ta hudu (salloli 15 kenan). Amma a wasu Maz’habobin tun daga ranar Arfa ake fara zikiran.

Bukhari ya fitar da Hadisin da aka karbo daga Ibn Abbas, hadisi ne ingatacce. An karba daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “babu wadansu kwanaki da aiki mai kyau a cikinsu suka fi soyuwa ga Allah daga wadannan kwana goma”. Kila Abdullahi Ibn Abbas ya fassara da cewa, Annabi (SAW) yana nufin wadannan kwana goman na farkon Zulhajji. Sai Sahabbai suka tambayi Manzon Allah (SAW) cewa, yanzu ko yaki don daukaka addinin Allah aiki a cikin wadannan kwana goman ya fi shi? Manzon Allah (SAW) ya ce ko shi ne. Sai dai yakin da mutum ya fita da ransa da dukiyarsa kuma ya yi shahada bai dawo ba, wannan ne kadai ya fi aiki a cikin wadannan kwanakin goma. Ma’ana ban da yakin da aka yi nasara aka samu ganima da sauransu. Shi ya sa Malamai suka sha wuya wurin bambance falalar Badar da Ukhudu. Badar an yi nasara, an samu ganima kuma Allah ya yaba da wadanda suka halarta har ya yi musu wata daraja ta daban, amma kuma Ukhudu an sha wuya da sauransu. To in aka dubi wannan Hadisi na falalar yakin da mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo ba, sai a ga Ukhudu ta fi Badar. To amma kuma Badar falala ce da Allah ya ba ta.

Labarai Masu Nasaba

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

Yanzu magana ta zama biyu, akwai maganar falalar wadannan kwanukan da kuma falalar aiki a cikinsu. Wannan Hadisi ya nuna aikin da aka yi a cikin wadannan kwanuka goma ya fi na duk wanda aka yi a cikin wasu da ba su ba a cikin shekara kaf, ba tare da coge kowanne ba. Idan kuwa Allah ya fi son aiki a cikin wadannan kwanukan, to su kansu kwanukan ma sun fi soyuwa a wurin Allah Tabaraka wa Ta’ala. Ya zo a cikin Hadisi da wannan lafazi, “Babu wasu kwanaki da aiki a cikinsu ya fi daga wadannan kwanaki goma”. Wannan Hadisi na biyu mai ruwaya ya ruwaito shi da shakku a cikin lafazin tsakanin “mafi soyuwa ko mafi falala” amma wancan Hadisin na sama ingatacce ne kuma ya ishe mu. Idan aiki a cikin wadannan kwana goma ya fi, kuma ya fi soyuwa a wurin Allah a cikin duk sauran kwanuka; to kenan falalar na kwanukan ne ba na aikin ba, domin aikin ana iya yinsa a wasu kwanukan da ba su ba amma kuma falalarsa ba zai kai na wadannan kwana goman ba. Saboda haka ne Sahabbai suka yi wancan tambayar ta sama da muka kawo.

Kowane irin aiki na alheri a cikin wadannan kwana goman yana da wannan falala. Sai dai kuma, za a iya cewa aikin farilla ya fi duk wata nafila, kenan aikin farillar da aka yi a wasu kwanukan da ba wadannan ba sun fi nafilar da aka yi a cikinsu? Eh, haka ne, to amma kuma su ma a cikin wadannan kwanukan goma akwai aikin farillar, don haka su sun fi farillar da aka yi a wasu kwanukan na daban. Nafilolin da aka yi a cikin kwanukan goma na farkon Zulhajji kuma sun fi wadanda aka yi a wasu kwanukan na daban.

Ya zo a Hadisin Ibn Abbas (RA) (dadi a kan wancan Hadisi da ya fada na sama), cewa, “aiki a cikin wadannan kwanukan goma ana ninka shi (falalarsa) sau dari bakwai”, sai dai madogarar wannan karin (na Hadisi) yana da rauni. Idan Sahabbai suka ruwaito magana ta Annabi (SAW) kowa aka ga ya tsaya a karshen wata magana bai-daya, idan aka samu kari daga wani, in Hadisin ingatacce ne to za a hada shi da karin, sai a ce kari ne na alheri. Amma idan akwai dan dugudugu a cikin madogarar Hadisin, galibi Bukhari ba ya yarda da Hadisin. Amma sauran masu Hadisi za su iya kawowa, sai kuma su ce ga kari da wane ya kawo, illa dai kuma Ahmdu bin Hambal ya ce wannan raunannan karin ya fi ingataccen kowane malami. Ma’ana ba yarwa za a yi ba, illa dai idan an ga akwai rikici ne da zai sa a yar da Hadisi ingatacce to sai a kyale shi kawai. Da yawa masu karatun yanzu, da sun ji an ce Hadisi raunanna ne sai su ce a yar da shi, a’a, ba haka abin yake ba. Wannan da aka ce raunanna ne ba a lafazin ba ne, daga mazajen Hadisin ne. Allah ya saka wa Malaman Hadisi da alkhairi da suka fitar mana da wannan. An tambayi Shehu Ibrahim Inyass (RA) shin wai wannan magana ta (tantance karya da gaskiya da Malaman Hadisi suke yi) ba nau’i ce ta gulma ba, Shehu ya ce, a’a, Malaman suna kare wa Annabi (SAW) ne. Malaman Hadisi suna iya yabon mai ruwaya su ce mai sallah ne, mai ibada ne amma da zarar ya yi santsi kan wani abu a cikin Hadisi sai su ce ba gaskiya ba ne, su raunana shi, saboda kiyaye Hadisan Manzon Allah (SAW).

To wannan ragowar (kari na) Hadisin Ibn Abbas (RA) bai inganta kamar na saman da aka fara kawowa a farko ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FalalaGoman FarkoZulhijja
ShareTweetSendShare
Previous Post

Duk Ɗan Nijeriya Da Ke Amfani Da Shafukan Intanet Na Shan Aƙalla Datar 9G Kowonne Wata

Next Post

GORON JUMA’A

Related

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Dausayin Musulunci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

2 weeks ago
Ramadan
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

3 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

4 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

1 month ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)

1 month ago
Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
Dausayin Musulunci

Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu

2 months ago
Next Post
GORON JUMA’A

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

May 14, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

May 14, 2025
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

May 14, 2025
Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

May 14, 2025
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

May 14, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

May 14, 2025
Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

May 14, 2025
Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

May 14, 2025
Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.