‘Yan Nijeriya na dokin ganin yadda farashin man fetur zai karye a kasar nan yayin da
dillalan man fetur suka fara shirin dakon mai daga matatar mai ta Fatakwal da ta Dangote bisa umarni daga Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL).
Dillalan sun shaida cewar suna sa ran matatar man Fatakwal da ke Jihar Ribas za ta fara sayar da man fetur a kan Naira 500 kan kowace lita.
- Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
- Yadda Wasu Tagwaye Suka Kirkiri Murhun Dafa Abinci Mai Amfani Da Ruwa Da Fetur
Sun sake bayyana fatansu na ganin farashin man ya sake karyewa, yayin da nan bada jimawa ba ake sa ran matatar mai ta Dangote za ta fara fitar da man fetur, bayan a baya-bayan ta fara sayar da man dizal ga ‘yan kasuwar cikin gida.
Kungiyar dilallan man fetur (IPMAN), ta hannun mai magana da yawunta, Ukadike Chinedu, ta bayyana cewar tuni dilallai suka fara shirye-shiryen fara dakon man fetur daga matatun man na Fatakwal da kuma Dangote tare da tunanin farashin da za su kayyade masa.
A cewarsa a yanzu NNPCL na bai wa dilallai man fetur a kan farashin Naira 567 kan kowace lita, amma a cewarsa suna fatan matatar man fetur ta Fatakwal za ta ba su a kan kasa da Naira 500.
An Fara Samun Dogayen Layuka A Gidajen Mai
A gefe guda kuma idan aka yi duba, za a ga an fara samun layi a gidajen mai a wasu sassan Nijeriya, watakila hakan na da nasaba da hasashen da ake yi na cewar farashin man fetur da dizal zai karye.
Wannan dai na daga cikin hasashen da ‘yan kasuwa da sauran masana kan harkar tattalin arziki da abin da masu fashin baki suka yi na cewar farashin zai karye matukar matatun man fetur na Dangote da Fatakwal suka fara bayar da mai.
A yanzu haka wasu gidajen mai na sayar da shi a kan Naira 700 zuwa 730. A wani bincike da LEADERSHIP Hausa ta yi a Jihar Kano, ta gano wasu gidajen mai na ‘yan kasuwa irin su AA Rano, AY Mai Kifi, Attaslim, Fara-Fara dukkaninsu na sayar da man fetur din ne kan farashin Naira 730 zuwa 780 a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar 15 ga watan Maris, 2024 shugaban kamfanin man fetur na kasa, Mallam Mele Kyari ya bayyana cewar matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki cikin makonni biyu masu zuwa.
A wancan lokaci ya jadadda cewar matatar ta Fatakwal, Warri an kammala dukkannin wasu manyan ayyukan da suka rage, yayin da ya ce ita matatar man fetur ta Kaduna za ta fara aiki a watan Disamban 2024.
Kyari, ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin majalisa da ke kula da harkokin man fetur kan halin da ake ciki game da fara aikin matatun man da aka jima ana dako.
Kyari ya shaida wa kwamitin cewar an sauke gangar mai 450,000 a matatar mai ta Fatakwal domin fara aiki a lokacin.
Dangote Zai Iya Karya Farashin Man Fetur Bayan Rage Na Dizal Da Man Jirgi
Dillalan man fetur suna jiran man fetur daga matatar mai ta Dangote ya shiga kasuwar cikin gida a hukumance, wanda suke fatan samun sa a farashin kasa da Naira 500 kan kowace lita. ‘Yan kasuwar suna wannan fata ne ganin yadda Dangote yake karya farashin man dizal, a watan Maris daga Naira 1,600 kan kowace lita zuwa Naira 1,200, yayin da kuma ya sake rage farashin dizal din daga Naira 1,200 zuwa Naira 1,000 kana bayan mako biyu da sanar da hakan, a wannan makon kuma ya sake sanar da rage farashin daga Naira 1000 zuwa 940, sannan ya sake sanar da rage farashin man jirgi zuwa Naira 980.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), Abubakar Maigandi, ya ce suna sa ran matatar man za ta sayar da man fetur a kan Naira 500 ko kasa da haka kan kowace lita. A cewarsa tagomashi da Naira ke samu kan Dalar Amurka shi ma na iya taka muhimmiyar rawa wajen sake karyewar farashin man fetur nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
“Idan dala ta ci gaba da karyewa, to farashin man fetur zai iya komawa farashinsa na asali.”
Shi ma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, yayin wata hira da manema labarai a Jihar Gombe, ya tabbatar da cewar farashin dizal zai dawo Naira 1,000.
“Wasu mutane sun rike kasuwanci na tsawon lokaci; sun jima suna cin kazamar riba amma mun yanke hukuncin za mu ke sayar da dizal kan Naira 1,000 wanda ke nuna an samu ragin kusan kashi 60 cikin dari. Yankuna kamar Gombe, Borno, Bauchi suna sayan dizal a kan Naira 1,700 zuwa 1,800 amma ‘yan kwanaki masu zuwa ba za ku sayi dizal sama da Naira 1,000 ba a duk fadin Nijeriya.
Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Mayun 2023, yayin rantsar da Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana dakatar da biyan tallafin man fetur, lamarin da ya sanya farashin man yin tashin gwauron zabi.
Hakan ne kuma ya sanya farashin kudin sufuri da kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi. Hakan ne ya san mutane da dama kokawa tare da yin kira ga shugabanni kan matsi da tsadar rayuwa da janye tallafin ya haifar.