Ministan Harkokin Kasuwanci da Tattalin arziki na kasar Faransa, Olibier Becht, ya ce, gwamnatin kasar Faransa na neman hanyoyin kara zurfafa harkokin kasuwanci da tarayyar Nijeriya musamman a bangaren ayyukan gona.
Becht ya bayyana haka ne a ranar Juma’a na makon jiya yayin da aka kaddamar da manhajar cinikayyar kayan abinci a tsakanin kasashen biyu.
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fito Da Manhajar DSO Na Aikin Talbijin Kwanan Nan – Minista
An samar da manhajar ne don saukaka wa al’ummar duniya gudanar da saye da sayarwa a kasuwannin kasar faransa da wasu kasashen Turai.
Ya kuma kara ca ewa, a yanzu za a samu sauki da bunkasar harkokin kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Faransa, musamman a bangaren saye da sayar da kayan gona.