Farashin man fetur a duniya ya yi tashin da bai taɓa yi ba a cikin watanni goma.
BBC ta rawaito cewa, Farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya tashi zuwa sama da dalar Amurka 95 a ranar Talata.
- Cire Tallafin Fetur: Zulum Ya Kaddamar Da Motoci 70 Don Saukaka Zirga-zirgar Al’umma.
- NLC Za Ta Gudanar Da Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 2 Kan Cire Tallafin Fetur
Tashin farashin ya zo ne bayan rage yawan ɗanyen man fetur da ƙasashe biyu mafiya fitar da man fetur ɗin suka yi, wato Saudiya da kuma Rasha.
Talla
Hukumar kula da makamashi ta duniya ta yi gargadin cewa ɗanyen man zai yi ƙaranci nan da ƙarshen shekara.
Farashin man fetur ya tashi zuwa dalar Amurka 120 kan kowace ganga bayan mamayen da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine a shekarar da ta wuce, sai dai ya sauko zuwa dalar Amurka 70 a cikin watan Mayu.
Talla