Daga Sulaiman Ibrahim
A karon farko a 2021, farashin mai ya tashi zuwa dala 71.28 a kowace ganga a kasuwar duniya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin taron ranar Alhamis inda Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC) da sauran mambobinta suka bijire wa matsin lamba kan kara yawan adadin gangar mai da suke samarwa.
Norbert Rücker, wani manazarci a bankin Switzerland Julius Baer, a ranar Laraba, ya bayyana cewa farashin mai na iya kaiwa sama da $ 70 kafin tsakiyar shekara.