Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa, farashin gas na girki na matsakaicin silinda mai nauyin kilogiram biyan ya kai naira 1,949.75 a watan Disambar shekarar 2020 daga naira 1,947.47 na watan Nuwamba. Hukumar NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na farashin gas a watan Disamsar shekarar 2020. A cewar NBS, a duk wata farashin silinda mai nauyin kilogiram biyan yana karuwa da kashi 0.12, wanda yake raguwa a duk shekara na kashi -3.41 a lokacin wannan kididdiga. Hukumar ta bayyana farashin silinda mai nauyin kilogiram na gas a wasu jihohin kasar nan, inda a Jihar Bauch ana sayar da shi kan naira 2,489.12, a Jihar Borno naira 2,396.69, Jihar Adamawa ana sayar da shi kan naira 2,392.88. Ta kara da cewa, jihohin da ake sayarwa da sauki dai sun hada da Jihar Inugu wanda ake sayarwa a kan naira 1,563.75, sai kuma Jihar Imo naira 1,678.89, sannan sai Jihar Oyo naira 1,691.67.
“Hakazalika, farashin silinda mai nauyin kilogiram 12.5 na gas din girki a gidajen mai yana karu da kashi 1.75 a duk wata bayan wata, sannan yana kuma raguwa da kashi -0.52 a shekara, inda ya kai naira 4,082.97 a watan Disamba daga naira 4,082.97 na watan Nuwambar shekarar 2020.
“Jihohin da suka fi tsada wajen sayar da gas na girki na silinda mai nauyin kilogiram sun hada da Jihar Delta wanda ake sayarwa a kan naira 4,838.46 da Jihar Kuros Ribas da Sakkwato wanda ake sayarwa kan naira 4,800 da kuma Jihar Akwa Ibom wanda ake sayarwa kan naira 4,614.49.
“Jihohin da suke da saurin farashi dai sun hada da Jihar Kaduwa wanda ake sayarwa a kan naira 3,191.67 da Jihar Zamfara wanda ake sayarwa kan naira 3,462.5 da kuma Jihae Nije wanda ake sayarwa kan naira 3,500,” in ji ta.