Abubakar Abba" />

Farashin Hatsi A Kasuwanni Ya Sha BamBan

Sakamakin binciken da aka gudanar akan wasu kayan abinci a wasu kasuwannin dake a kasar nan sun nuna cewa, farashin hatsi yasha ban-ban a wasu kasuwannin.

Rahotannin sun nuna cewa, farashin kayan abinci a wasu kasuwannin sun banbanta, inda a kasuwanni hakan farshin a hau a wasu kima farashin ya tashi.

A cewar rahoton, misali farashin buhun shinkafa yar Hausa mai tiya 40 a wannan makon a kasuwar Giwa dake a cikin Jihar Kaduna ya kai naira 27,000.

Bugu da kari, rahotin ya kara da cewa, a kasuwar Dandume dake a cikin jihar Katsina farashin na shinkafa yar Hausa ya kai naira 28,000.

Rahotannin har ila yau, sun kuma nuna cewa, farashin na shinkafar yar Hausa a kasuwar Mashi dake a cikin jihar Katsina, ya kai naira 19,000.

A cewar rahoton, a kasuwar Kara dake a cikin jihar Sokoto farashin buhun shinkafar yar Hausa ya kai naira 28,000.

Rahoton ya kuma ci gaba da cewa, har ila yau, a kasuwar Charanchi dake a cikin jihar Katsina farashin buhun shinkafar yar hausa ya kai naira 27,000, inda kuma a kasuwar cikin garin Gombe, farashin shinkafar ya kai naira 27,000.

Rahotin a karshe ya bayyana cewa, a wasu kasuwannin, rahotannin sun nuna cewa, farashin sauran kayan abinci kamar su, wake da masara da gero da gyada da alkama da dawa da waken soya da dai sauransu, suma farashin su ya bambanta.

Exit mobile version