Farashin Litar Fetur Zai Kai 340 Idan Aka Cire Tallafi A Shekarar 2022, Inji Kyari

Rabiul

Shugaban Kamfanin NNPC Mele Kyari ya ce farashin litar man fetur zai iya kaiwa naira N320 zuwa N340 daga farkon shekarar 2022. Kasa da mako guda kenan da hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF, ta baiwa gwamnatin Nijeriya shawarar cire tallafin man fetur domin karkata kudaden da take zubawa zuwa ayyukan raya kasa.

Kyari yace tabbas babu abinda zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin zata daina aiki daga karshen watan Fabrairu mai zuwa. Shugaban kamfanin man yace a shekara mai zuwa babu wani tanadi da akayi na sanya kudin tallafin, kuma ganin yadda ayyuka suka yi wa gwamnati yawa, zasu aiwatar da shirin janye shi a cikin sauki.

Dangane da tashin farashin iskar gas da ake girki da shi kuwa, Kyari yace batu ne na karuwar bukatar sa ta haifar da hauhawan farashin tare da karancin sa a kasuwannin duniya. Shugaban kamfanin NNPC yace dama iskar gas bashi da wani tallafin da gwamnati take sanyawa, saboda haka farashin sa na tafiya ne da yadda kasuwar duniya take a koda yaushe.

Exit mobile version