Dillalan Man Fetur a Nijeriya sun ce da yiwuwar farashin litar man fetur ka iya rayuwa zuwa tsakanin naira 900 ko 1,000, lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a bisa yunkurin matatar man Dangote.
Shugaban kungiyar masu sayar da mai a gidajen mai na kasa (PETROAN), Billy Gillis-Harry, da Kakakin kungiyar dillalan mai na kasa (IPMAN), Chinedu Ukadike, su ne suka shelanta hakan a ranar Litinin.
Wannan matakin na zuwa bayan da matatar man Dangote a ranar Lahadi ta rage farashin Litar mai da naira 20, inda ta dawo naira 970 daga naira 990 kan lita guda. Kamfanin ya yi bayanin cewa an yi hakan ne domin nuna godiya ga goyon bayan ‘yan Nijeriya.
Wannan kuma na zuwa ne bayan makonni da matatar ta sanya hannu da dillalai mai domin sayar musu da mai kai tsaye.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan, Gillis-Harry ya ce rigin farashin da matatar Dangote ta yi zai taimaki ‘yan Nijeriya sosai.
A cewarsa, da yiwuwar farashin ma zai ci gaba da sauka amma ya danganta ne da farashin danyen mai da kuma matatar Dangote.
“Tabbas farashin zai ci gaba da raguwa nan gaba. Abu ne mai kyau ga masu jan ragamar da ‘yan Nijeriya,” ya shaida.
Kazalika, shi ma Ukadike ya tsugunta wa ‘yan Nijeriya cewa farashin mai da rahusa na nan tafe a wannan lokaci bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ya bayyana cewa rage farashin man da matatar Dangote ta yi a baya-bayan nan ya nuna cewa farashin man fetur a duk gidajen mai na mambobin IPMAN zai ragu tsakanin naira 15 zuwa naira 20, ya dangane da wurin ko nisan gari.
Ukadike ya kara da cewa farashin man fetur mafi arha da ‘yan Nijeriya za su yi tsammani nan da Disamba 2024 ya kamata ya kasance tsakanin naira 900 zuwa naira 1000 kowace lita.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Juma’ar makon da ya gabata ne Kamfanin Mai na Nijeriya ya shaida wa ‘yan kasuwar man da su dakatar da shigo da mai su maida hankali kan matatar ta Dangote.