Jam’iyyar APC ta zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.
An zaɓe shi ne domin ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus a kwanakin baya.
- Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
- Yawan Ma’aikata Ne Ya Hana Borno Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi – Zulum
Farfesa Yilwatda yana riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin-ƙai a halin yanzu.
Kafin yanzu, malami ne a Jami’a kuma ya taɓa zama Kwamishinan zaɓe a hukumar INEC.
A shekarar 2023, ya tsaya takarar gwamna a Jihar Filato.
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC.
Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis.
Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar.
Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne.
Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp