Khalid Idris Doya" />

Fashewar Tankar Mai Ya Kashe Mutum 50, 70 Sun Jikkata A Binuwe

A kalla mutane hamsin 50 ne aka rawaito sun rasa rayukansu a shekaran jiya da yamma a sakamakon fashewar tankar mai a wani kauye da ke Ahumbe da ke karamar hukumar Bwer a jihar Binuwai sa’ailin da motar ke kokarin jigilar man fetur.

Wakilin jaridar Leadership ya nakalto cewar tankar wacce ta kwaso man fetur daga Aliade ta gamu da hatsari ne a daidai wani kauye da ake kira da Ahumbe inda man da tankar ke dauke da shi ya fara tsiyaya lamarin da ya haifar da fashewar tankar da ta jawo kamawa da wuta wanda har hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar Gwer ta gabas, Christopher Abi a lokacin da ke zantawa da wakilinmu ta wayar tarho ya tabbatar masa da mutuwar mutane 50 wadanda wutar ta konesu kurmus, kana mutane 70 sun gamu da munanan raunuka a sakamakon wannan hatsarin wanda aka kwashesu zuwa asibitoci daban-daban domin ceto rayukansu.

Kamar yadda Abi ke shaidawa, wadanda tsautsayin ta fada musu, suna kokarin fitar da man daga cikin tankar ne wutar ta fashe da su.

Jami’in ya shaida cewar da dama daga cikin wadanda tsautsayin ya shafa mazauna wannan kauyen da tankar ta fashe a wurin ne.

Ya kuma kara da cewa gidaje da daman gaske ne suka kone kurmus bayan da wutar ta fantsama zuwa garesu.

A lokacin da muka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ta tabbatar da aukuwa lamarin, amma ta shaida cewar a daidai wannan lokacin ba za ta iya shaida mana hakikanin mutane nawa ne suka mutu da wadanda suka jikkata a daidai wannan lokacin da muka tuntubeta ba.

Ta shaida cewar wadanda suka gamu da raunuka an harnzatar kaisu zuwa asibiti domin ceto rayukansu daga wannan hatsarin.

Kawo lokacin hada wannan rahoton da muka iya jin ta bakin hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar ba.

Exit mobile version