Fayose Ya Mayarwa Da Adesina Martani

Naga maganganun dan uwana kuma abokina Femi Adesina, inda yake cewa; ‘Shugaban Kasa Buhari ya kyalemu ne, bai yi maganin mu ba, ni da Gwamna Wike.’ A nawa ra’ayin Shugaban Kasa Buhari, ya zama shugaban kasa ne bisa hatsari, sannan bai ma san mene yake faruwa a kewaye da shi ba, mutumin da ya gaza kare rayuwar al’ummar mahaifarshi, bai wuce mutum-mutumi ba.

In ba haka ba, ya za ayi hadimanshi su dinga cewa ya hukunta ‘yan Nijeriya kamar wasu bayinshi, in ka lura Femi Adesina kwana biyu na kame bakina, saboda na fahimci shugabancin Buhari na summum bukumun ne.

Ina mai shawartarka da ka kada ka tsokano ni, saboda tabbas zaka tsokano abinda yafi karfinka.

Exit mobile version