Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Fetur Da Lantarki: Babu Sauran Kudaden Tallafi – Ngige

by Muhammad
February 24, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ministan kwadugo da ayyuka, Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa, babu wani sauran kudaden tallafin mai da na wutar lantarkin da gwamnatin tarayya za ta kara biya. Ya bayyana ce, gwamnatin tarayya ta shawarci kungiyar kwadugo da ta jira hukunci na karshe da za ta zantar bayan ta gana da gwamno36 da ke fadin kasar nan a ranar Alhamis. Wannan ya biyo bayan karuwar farashin gangan danyan mai a kasuwan duni zuwa dala 60. Shi dai man fetur ana samun sa ne bayan an tace danyan mai.

An gyara bangaren mai tun a wata Maris ta shekarar 2020 lokacin da farashin kowacce gangan danyan mai yake kan dala 40 a kasuwan duniya. Shugabannin kwadugo da na kugiyar ‘yan kasuwa sun tattauna da gwamnatin tarayya a kan ta rage kudin farashin man fetur da ake sayarwa a gidajan mai.

Ngige ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawa tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadugo a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ngige ya bayyana wa manema labarai cewa, za a gudanar da bincike a kan rahoton kwamitin farashin mai wanda aka amince subayar a karshen taron da aka gudanar, ko kamfanin mai ta kasa za ta bayaar da nata rahoton.

Ya ce, “bangaren kungiyar kwadugo ya amince da wasu bayanin da kamfanin mai ta kasa ya gabatar, amma kamar yadda na fadi a baya ana kan aiki a kan lamarin. Gwamnoni za su tattauna a kan haka a ranar Alhamis. An tattauna lamarin a wajen taron majalisar zantarwa kuma kowa ya shiga cikin lamarin saboda mun tsinci kansu a cikin mayuyacin hali.

“Gyara fannin mai kamar dai dogara ne da shigo da man amma suna samun nasarar sayarwa da yawa. Ta haka ne suke yin ragi. Haka kuma ana musu ragi wajen canjin  kudade. Ba sa yin canjisu daga hannun ‘yan kasuwa. Dole ne a yi  la’akari da wadannan abubuwa wajen kayyade farashi,” in ji shi.

Ministan ya kara da cewa, taron ya amince da rahoton kwamitin karin farashin kudin wutar lantarki, amma yana bukatar a yi masa wasu gyare-gyre kafin a amince da haroton kawaminin tare da na bayar da mita.

“Za ku fara ganin mambobin kwamitin da ministan wutar lantarki suna zagayawa wajen tabbataar da kamfanonin rarraba wutar lantarki sun bai wa mutae mita saboda ya rahoton ya nuna cewa akwai wadanda ba sa son rarraba mitan sai dai su dunga bayar da kudin wutar da ba a kayyade ba. Kuma ba ma bukatar hakan,” in ji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Dakatar Da Saida Layukan Waya Ya Kara Ruruta Wutar Rashin Aiki – Kwararru

Next Post

Yadda Za A Samar Da Abinci Mai Yawa A Nahiyar Afirka

RelatedPosts

Emefiele

Bunkasa Tattalin Arziki: Nijeriya Na Bukatar Kara Kaimi Wajen Adana Abinci – Emefiele

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN),...

Bankuna

Rahoton Bangaren Bankuna Yana Nuna Samun Cigaba Mai Matukar Ma’ana – CBN

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Rahoton karshe na Babban bankin...

Gwamnatin Masar

Lantarki: Nijeriya Za Ta Hada Kai Da Masar

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya...

Next Post
Nahiyar Afirka

Yadda Za A Samar Da Abinci Mai Yawa A Nahiyar Afirka

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version