Hedikwatar tsaro ta kasa, ta musanta rahotannin da ke cewa; Jamhuriyar Nijar ta fice daga cikin rundumar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), inda ta bayyana cewa; wannan mataki ne da ka iya haifar da babbar illa ga tsaron kasashen biyu.
Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasar, ta kunshi rundunonin soji daga kasashen Benin, Kamaru, Chadi, Nijar da kuma Nijeriya. Hukumar kula da tafkin Chadi (LCBC) ce ta kafa shi a watan Maris na shekarar 1994, domin yaki da rashin tsaro a yankin.
- Sin: Idan Har Amurka Na Son Tattaunawa, Ya Zama Wajibi Ta Dakatar Da Aiwatar Da Matakan Gangaci
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Daraktan Yada Labarai na Hukumar Tsaro, Manjo Janaral Markus Kangye ya bayyana cewa; rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), na nan kamar yadda aka santa wajen hadin gwiwa a fannin tsaro a yankin, kazalika dole ne kuma a yi kokarin hana kowace kasa a matsayinta na mamba ficewa.
Ya nanata cewa, daukar irin wannan mataki ko kadan ba zai taimaki Nijeriya ko Jamhuriyar Nijar ba.
Ya ce, “Ai ina ganin wannan abu ne da aka dauki tsawon wasu watanni ana tattaunawa akansa, musamman lokacin da wasu mambobin ECOWAS, suka yanke shawarar kulla kawance da kuma yunkurin ficewa daga ECOWAS.
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji.
Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu.
Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka.
Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin sama da wasu manyan hafsoshi daga hedikwatar hukumar suka ziyarci sojojin, domin taya su murnar Sallah.
“Sannan kuma, zan iya fada muku cewa; hedikwatar rundunar sojojin Nijeriya, na kula da marasa lafiya da wadanda suka samu raunuka da wasu da ke bukatar a fitar da su zuwa kasashen waje, ana fitar da su, domin nema musu lafiya; wasu sun tafi Masar, wasu Turkiyya, wasu kuma Kasar Indiya. Kamar yadda muke magana yanzu, wasu har yanzu suna can suna samun kulawar likitoci a can.”
Ya kuma bayyana cewa, a ‘yan watannin da suka gabata, an raba wa sojojin da suka samu jikkata a fagen-daga gidaje.
Kangye ya kuma yi nuni da cewa, an raba wa sojojin da suka jikkatan gidajen kyauta ne, domin kuwa wasu daga cikinsu; ba za su iya dawowa fagen aiki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp